An kashe mutum 2 a Taraba kan shugabancin masallacin Jumma'a
Jaridun Nijeriya sun ambato wata majiya daga garin da ke cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin Musulman garin kan wanda zai ja sallah a babban masallacin garin.
An kashe aƙalla mutum biyu a wani rikici kan shugabancin babban masallacin garin Donga da ke Jihar Taraba a arewa maso gabashin Nijeriya.
Rahotanni daga yankin sun ce wasu mutane sun ji rauni a rikicin sannan an lalata wasu gidaje.
Jaridar Daily Trust ta Nijeriya ta ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne ranar Talata kan limancin babban masallacin Donga wanda ke ƙofar gidan sarkin garin.
Jaridar ta ambato wata majiya daga garin da ke cewa rikicin ya ɓarke ne tsakanin Musulman garin kan wanda zai ja sallah a babban masallacin garin.
Wannan ya janyo arangama tsakanin ƙungiyoyi biyu.
Majiyar ta bayyana cewa an tura jami’an tsaro ciki har da sojoji domin dawo da zaman lafiya a yankin.
Jaridar ta ce ƙoƙarinta na tuntuɓar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Leshen James, game da lamarin ya ci tura.