Rundunar sojin Isra'ila na fuskantar mafi munin matsalar ƙarancin ma'aikata a tarihinta - Janar Brik

Babban Janar kuma mai sharhi kan harkokin soji na Isra'ila Itzhak Brik ya ce mummunan halin da rundunar sojin Isra’ila ke ciki na iya haifar wa ƙasar "rasa ikonta na aiki gaba ɗaya."

By
Sojojin Isra'ila na fama da "makanta ta bayanai" saboda tsohon tsarin da kuma durkushewar tsarin bayanai, in ji shi. / Reuters

Rundunar sojin Isra'ila na fuskantar “mafi munin matsalar rashin ma'aikata a tarihinta” a yayin da ake fama da ƙarancin dakaru, a cewar wani babban Janar Kana, mai sharhi kan harkokin rundunar sojin Isra'ila Itzhak Brik.

A wani sharhi da ya yi a Jaridar Maariv ta yau da kullum, Brik ya ce dubban jami'ai da dakarun ko ta-kwana sun guji sadaukar da kai ga aikin a ‘yan watannin baya bayan nan, ko dai ta hanyar ƙin amsa kiran da aka yi musu ko kuma kin sabunta kwangilolinsu.

A shekaru biyu na yakin kare dangi na Isra'ila a Gaza, rundunar sojin ƙasar ta rasa sojoji 923 yayin da 6,399 suka jikkata, sannan kimanin sojoji 20,000 ne ke fama da matsalar damuwa bayan tashin hankali (PTSD), a cewar kafofin watsa labarai na Isra'ila waɗanda suka tattaro bayanan daga sojojin.

A ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro na sojin, rundunar sojin na fuskantar zarge-zargen boye asarar da ta yi masu yawa don karfafa gwiwarta.

Brik ya rubuta cewa jami'ai da yawa sun nemi sallama nan take, sannan sabbin matasa da aka dauka aiki sun ƙi sanya hannu kan kwangila ta tsawon lokaci, wanda hakan ya haifar da ƙarancin ma'aikata a faɗin rundunar.

Ya ƙara da cewa, raguwar yawan jami’an ya matukar raunana kula da kayan aiki da kuma tsarin yaki na ƙasar.

Masanin harkokin sojin ya yi gargaɗi cewa halin da ake ciki na iya sanya nan gaba kaɗan rundunar ta '‘rasa ikon yin aiki gaba ɗaya.'‘

'Durƙushewar tsarin baki ɗaya’

Ya zargi shugabannin rundunar na baya da 'daukar munanan shawarwari’ a 'yan shekarun da suka gabata, ciki har da rage ma'aikata da kuma takaita wa'adin aiki - shekaru uku ga maza, sai kuma shekaru biyu ga mata - lamarin da ya ce ya haifar da "babban gibi da ba za a yi saurin cike wa ba."

Wadannan gibin 'sun tura kwararru da suka goge daga aikin yi wa ƙasa hidima yayin da suka bar jami’ai da ba su kwarewa a mukamai masu muhimmanci don su tinkari ƙalubalen yanzu da ake fuskanata a fagen daga, in ji shi.

Brik ya ce sashen ma'aikatan rundunar ya shafe shekaru yana aiki "ba tare da ƙwarewa ko nauyi ba" kuma ya yi watsi da manyan matsalolin kula da albarkatun ɗan adam da tantance buƙatunsa.

Sojojin suna fama da "makanta ta bayanai" saboda tsohon tsarin da kuma durkushewar tsarin bayanai, in ji shi.

Brik ya yi gargaɗin cewa matsalar arancin ma’aikata zai iya haifar da "ɗurkushewar tsarin baki ɗaya" na sojojin Isra'ila.

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da 70,000, waɗanda mafi yawan su mata da yara ne, a kisan gillar da ta yi a Gaza tun daga watan Oktoba na 2023.

Ta mayar da mafi yawan yankunan zuwa kango, sannan kusan dukkan al’ummar yankin sun rasa matsugunansu, lamarin da ya tilasta musu yin gudun hijira.