A halin yanzu ƙasar da take ta ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon ƙafa a jadawalin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, Faransa tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suke da damar lashe gasar inda Kylian Mbappe ke gaba-gaba cikin jerin ‘yanwasan kocinta Didier Deschamp.
Zai haɗu da wasu irin su ‘yanwasan gaba Ousmane Dembele da Michael Olise, da ‘yanwasan tsakiya Aurelien Tchouameni da N'Golo Kante, da ‘yanwasan baya su William Saliba da Jules Kounde da Theo Hernandez da gola Mike Maignan.
Sunan Camavinga bai fito ba a cikin jerin sunayen ‘yanwasa 26 duk da cewa yana cikin ‘yanwasan da suka kai Faransa wasa na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022. An kira shi domin buga wasannin sada zumunta na watan Maris, amma an tsallake shi domin gayyato ɗan wasan Real Madrid Thiago Pitarch.
"Ya samu kaka mai cike da matsala inda ya yi wasanni kaɗan. Ya kuma ji raunuka ," kamar yadda Deschamps ya bayyana . "Gaskiya ne cewa ɗan wasa ne da ya fara wasa fa sauri-sauri tare da mu. Har yanzu danwasa ne matashi.
"Saboda ina da zaɓuka da za ni yi domin samun daidaito wajen gina jerin ‘yanwasa da kuma daidatio a cikin ‘yanwasan baya da na tsakiya da na gaba. Amma na gane kuma za ni iya jin ɓacin ransa mai yawa a wannan yammaci."
Deschamps ya kuma zabi tafiya da ɗanwasan Rennes Brice Samba da ɗan wasan Lens Robin Risser, wanda aka ayyana a matsayin golan da ya fi iya wasa a gasar Ligue 1 ta wannan kakar, a matsayin safiya na Maignan.
Wannan na nufin za a bar Lucas Chevalier, wanda ya rasa gurbi na farko a Paris Saint-Germain ga Matvei Safonov a farkon wannan shekarar.
Iya wasa
"Muhimmin sharaɗi shi ne iya wasa ," kamar yadda Deschamps ya bayyana . "Na fahimci cewa Lucas Chevalier zai iya ɓata rai, amma bai yi wasan ba na tsawon watanni . A lokacin da zai iya samun lokacin yin wasa bai yi wani wasa ba ."
Faransa za ta yi wasannin sada zumunta na gabannin gasar cin kofin duniya da Ivory Coast da kuma Northern Ireland kafin ta tafi sansaninta na gasar cin kofin duniya a Boston. za su fara wasanninsu na rukuni I ne da Senegal ranar 16 ga watan Yuni kafin su yi wasanni da Iraƙi ranar 22 ga watan Yuni da kuma Norway ranar 26 a watan Yuni.
"Akwai ababen da ake tsammani da kuma ake nema , da gaske ," kamar yadda Deschamps ya bayyana . "Wannan ma laifinmu ne , saboda idan muna inda muke a yau, saboda mun yi nasara a wasanni ne -- fiye da abokan gabanmu.
“Cewa muna cikin ƙasashen da ake ganin sun fi kowa damar lashe gasar abu ne na ɗabi’a, amma akwai wasu tawagogi na daban . za ni iya ambato guda shida ko bakwai.
"Wannan gasar cin kofin duniya ce, gasa mafi girma daga cikinsu gabaɗaya. Tawagogi da suka fi ƙarfi ne ke ciki."
Sauran sanannun ‘yanwasa biyun da ba sa cikin jerin sunayen ‘yanwasan na ƙarshe su ne ɗanwasan Tottenham Randal Kolo Muani da ɗanwasan Rennes Esteban Lepaul, ɗanwasan da ya fi zura ƙwallaye a raga a gasar Ligue 1.
Ɗanwasan Crystal Palace Jean-Philippe Mateta yana cikin jerin ’yanwasan duk da cewa ba a saka shi a wasan sada zumunta na watan Maris ba saboda raunin da ya ji a gwiwa.
Zai kuma taimaka wajen cike gurbin da rashin Hugo Ekitike sakamakon ciwon a bayan ƙafa ya bari.
Wannan zai kasance gasar ƙwallon ƙafa ta ƙarshe ga Deschamps, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa lashe gasar cin kofin ta shekarar 2018.
Ana tsammanin cewa tsohon gwarzon tawagar ƙasar Zinedine Zidane ne zai maye gurbinsa.
Farasa ta kuma lashe gasar cin kofin duniya ta shekarar 1998.
Jerin sunayen ‘yanwasan Faransa a gasar cin kofin duniya
Gololi: Mike Maignan (AC Milan), Robin Risser (Lens), Brice Samba (Rennes)
‘Yawasan baya: Malo Gusto (Chelsea), Maxence Lacroix (Crystal Palace), Jules Kounde (Barcelona), Lucas Digne (Aston Villa), Ibrahima Konate (Liverpool), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich), Lucas Hernandez (Paris Saint-Germain), Theo Hernandez (Al Hilal)
‘Yanwasan tsakiya: Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Adrien Rabiot (AC Milan), N'Golo Kante (Fenerbahce), Manu Kone (Roma), Warren Zaire-Emery (Paris Saint- Germain)
‘Yanwasan gaba: Ousmane Dembele (Paris Saint-Germain), Bradley Barcola (Paris Saint- Germain), Jean-Philippe Mateta (Crystal Palace), Rayan Cherki (Manchester City), Marcus Thuram (Inter Milan), Maghnes Akliouche (Monaco), Desire Doue (Paris Saint-Germain), Kylian Mbappe (Real Madrid), Michael Olise (Bayern Munich).









