| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
Jami'in ɗansandan ya rasu ne bayan bindigarsa ta samu matsala a yayin musayar wuta da 'yanbindiga a yankin Karamar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina.
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
Tuni aka aika da gawar jami’in da ya rasu zuwa Zariya da ke Jihar Kaduna, domin yi masa jana’iza. / Reuters
16 awanni baya

‘Yan bindiga sun kashe DPO na ‘yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir, yayin wani samame da ‘yansandan suka kai kan waɗanda ake zargi da satar shanu, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an hallaka ‘yanbindiga uku a yayin farmakin hadin gwiwa da jami’an tsaro da kuma al’ummar yankin suka gudanar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya fitar, ya bayyana alhinin rasuwar jami’in, wanda aka kashe yayin da yake jagorantar aikin.

Sanarwar ta ce an samu sahihan rahotanni da daddare daga shugabannin al’umma a Karamar Hukumar Rimi, ciki har da kansilan mazaba, ‘yan jam’iyyar APC, mai unguwar Karare da kuma hakimin Rimi, kan kasancewar wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne da nufin satar shanu a garin Magaji da ke Mazabar Maje-Gobir. Bayan tabbatar da rahoton, DPO din nan take ya tattara jami’an tsaro zuwa yankin.

An ce ‘yanbindigar sun kai farmaki Magajen Gobir, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tunkare su. Artabun ya ci gaba har zuwa asubahi, a daidai lokacin Sallar Asuba, inda aka samu nasarar kwato mafi yawan shanun da aka sace.

Sanarwar ta kara da cewa a wasu artabun da suka biyo baya a yankunan makwabta, an harbe wasu maza biyu da kuma wasu ‘yan mata da dama, duk da cewa an sake kwato yawancin dabbobin da aka sace sakamakon hadin gwiwar mazauna yankin da jami’an tsaro.

“Daga bisani, jami’an tsaro tare da taimakon ‘yan sa-kai na yankin sun sake fafatawa da ‘yan bindigar, inda DPO din ya jagoranci aikin da kansa. A yayin musayar wuta, bindigarsa ta samu matsala kuma daya daga cikin ‘yan bindigar, wanda aka ce shi ne jagoransu mai suna Maigemu, ya harbe shi har lahira,” in ji Mu’azu.

Ya kara da cewa jami’an tsaro uku da suka jikkata na jinya a Asibitin Koyarwa na Katsina, yayin da aka kai gawar jami’in da ya rasu zuwa Zariya da ke Jihar Kaduna, domin yi masa jana’iza.