| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
Jami'in ɗansandan ya rasu ne bayan bindigarsa ta samu matsala a yayin musayar wuta da 'yanbindiga a yankin Karamar Hukumar Rimi ta Jihar Katsina.
'Yanbindiga sun kashe DPO na 'yansandan Nijeriya a Jihar Katsina
Tuni aka aika da gawar jami’in da ya rasu zuwa Zariya da ke Jihar Kaduna, domin yi masa jana’iza. / Reuters
14 Fabrairu 2026

‘Yan bindiga sun kashe DPO na ‘yan sanda mai kula da Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, CSP Muhammad Sani Kabir, yayin wani samame da ‘yansandan suka kai kan waɗanda ake zargi da satar shanu, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta tabbatar da cewa an hallaka ‘yanbindiga uku a yayin farmakin hadin gwiwa da jami’an tsaro da kuma al’ummar yankin suka gudanar.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya fitar, ya bayyana alhinin rasuwar jami’in, wanda aka kashe yayin da yake jagorantar aikin.

Sanarwar ta ce an samu sahihan rahotanni da daddare daga shugabannin al’umma a Karamar Hukumar Rimi, ciki har da kansilan mazaba, ‘yan jam’iyyar APC, mai unguwar Karare da kuma hakimin Rimi, kan kasancewar wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne da nufin satar shanu a garin Magaji da ke Mazabar Maje-Gobir. Bayan tabbatar da rahoton, DPO din nan take ya tattara jami’an tsaro zuwa yankin.

An ce ‘yanbindigar sun kai farmaki Magajen Gobir, lamarin da ya sa mazauna yankin suka tunkare su. Artabun ya ci gaba har zuwa asubahi, a daidai lokacin Sallar Asuba, inda aka samu nasarar kwato mafi yawan shanun da aka sace.

Sanarwar ta kara da cewa a wasu artabun da suka biyo baya a yankunan makwabta, an harbe wasu maza biyu da kuma wasu ‘yan mata da dama, duk da cewa an sake kwato yawancin dabbobin da aka sace sakamakon hadin gwiwar mazauna yankin da jami’an tsaro.

“Daga bisani, jami’an tsaro tare da taimakon ‘yan sa-kai na yankin sun sake fafatawa da ‘yan bindigar, inda DPO din ya jagoranci aikin da kansa. A yayin musayar wuta, bindigarsa ta samu matsala kuma daya daga cikin ‘yan bindigar, wanda aka ce shi ne jagoransu mai suna Maigemu, ya harbe shi har lahira,” in ji Mu’azu.

Ya kara da cewa jami’an tsaro uku da suka jikkata na jinya a Asibitin Koyarwa na Katsina, yayin da aka kai gawar jami’in da ya rasu zuwa Zariya da ke Jihar Kaduna, domin yi masa jana’iza.

 

 

Rumbun Labarai
'Yanta'addan ISWAP sun kashe sojojin Nijeriya 14 a hare-hare biyu
Tinubu ya ba da umarnin fitar da kudi nan-take don gyara kayan aikin sararin samaniyar Nijeriya
Nijeriya ta tara fiye da naira tiriliyan biyu daga harajin VAT a wata uku na karshen 2025 – NBS
'Yanbindiga sun raba fiye da mutum 300,00 da gidajensu a jihar Neja – Gwamna Bago
Ramadan: INEC ta sauya ranakun zaɓen 2027
An kashe aƙalla mutum 25 a wani hari da ake zargin Boko Haram da kai wa a Jihar Adamawa a Nijeriya
Hare-haren ƙungiyoyin 'yanta'adda kan iyakokin Nijar, Benin da Nijeriya na ƙaruwa: Bincike
Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na 'yansandan Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin biyan kudin fansa don ceto daliban Jihar Neja
'Yansandan Nijeriya sun kashe ɓarayin daji tare da kama mai safarar makamai a Kaduna
Tarayyar Afirka ta nemi a 'ɗauki mataki' bayan an kashe gomman mutane a Zamfara a Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun kashe 'yanta'adda 25 masu alaƙa da Daesh a jihar Borno
NDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi don ɓoye ƙwayoyi
Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta lashe zaɓukan cike gurbin da aka gudanar a Kano
Nijeriya: 'Yanbindiga sun kashe mutum 50 da garkuwa da wasu da dama a Jihar Zamfara
Hukumar NCDC ta Nijeriya ta tabbatar da samun mutum 318 ɗauke da zazzaɓin Lassa da mutuwar mutum 70
Gobara ta ƙona shaguna aƙalla 50 a Kasuwar Fatima Simra a Kanon Nijeriya
'Yansanda sun tabbatar da mutuwar mutum 33 a harin Kebbi
Dakarun Nijeriya sun kama mai 'kai wa Boko Haram jirage marasa matuƙa'
Mutane da dama sun rasa rayukansu a hare-haren Lakurawa a Jihar Kebbi a Nijeriya