| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Aƙalla mutane 518 ne suka mutu a zanga-zangar bayan zaɓe a Tanzania: Bincike
Kwamitin binciken ya ce ba a tabbatar da zarge-zargen binne mutane da yawa a waje guda ba, kuma hotunan da aka yaɗa a intanet an samar da su ne ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira (AI).
Aƙalla mutane 518 ne suka mutu a zanga-zangar bayan zaɓe a Tanzania: Bincike
FILE PHOTO: 'Yan sanda do sojoji sun kalubalanci masu zanga-zangar. / AP / AP

Kwamitin bincike da gwamnati ta kafa a ranar Alhamis ya ce rikicin zaɓe a ƙasar Tanzania a bara ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 518.

An ayyana shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen ranar 29 ga Oktoba da kashi 98 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa bayan da aka hana manyan 'yan adawa tsayawa takara.

Amma zaɓen ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar tsawon kwanaki da dama.

'Yan adawa da ƙungiyoyin addini sun ce an kashe dubban mutane, tare da rahotannin cewa an samu kaburburan da aka binne mutane da yawa da ƙwace gawarwaki daga ɗakunan ajiyarsu na asibiti.

Gwamnati ba ta bayar da wani adadi na waɗanda suka mutu ba har zuwa ranar Alhamis, kuma kwamitin ya gano cewa "ba za a iya tabbatar da zargin wanzuwar kaburburan da aka binne mutane da yawa ba".

‘Hotuna da aka ƙirƙira’

"Jimillar mace-macen da aka samu sakamakon babban zaɓen sun kai 518, waɗanda 490 daga ciki maza ne," in ji Mohamed Chande Othman, shugaban kwamitin da Shugaba Saluhu Hassan ta kafa, amma ya ce adadin "ba na ƙarshe ko kuma kammalalle ba ne".

"Hotunan da aka yaɗa a intanet, wasu daga cikinsu na gaske ne, yayin da wasu... an ƙirƙire su ne ta amfani da fasahar zamani ta AI," in ji Othman.

Katsewar intanet a lokacin da kuma bayan zaɓen ya rikitar da ƙoƙarin tabbatar da girman tashin hankalin.

'Yan adawa sun ce binciken "ba zai iya zama mai zaman kansa ko kuma marar son kai ba, musamman a yanayin da gwamnati ke kan gaba wajen aikata laifukan da ake bincike a kansu".

Tashin hankalin ya haifar da suka mai tsanani daga masu sa ido na Afirka, inda Tarayyar Afirka ta ce zaɓen bai bi ƙa'idojin zaɓen dimokuraɗiyya ba."

Rumbun Labarai
Me samar da lantarki ke nufi ga Afirka?
Chivayo: Rayuwar attajirin da ya mutu, wanda ya taba ba wa wani mawaki $1m don yin wasa a biki
Hare-haren 'yanta'adda sun kashe gomman sojoji a wurare biyu a Nijar
An zaɓi matasan Nijar 500 domin samun horo a kyauta don koyon sana’o’i a Aljeriya
Fiye da mutum 55,000 daga Sudan sun tsere zuwa gabashin Chadi don gudun hijira
Wasu karin mayakan RSF sun sauya sheka zuwa Rundunar Sojin Sudan bayan sun gamu da 'masifu'
Ana samun ƙaruwar Ƙasashen Yamma masu goyon bayan biyan diyyar cinkin bayi: Ghana
Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar
Zakuna goma sun mutu a wani gandun dabbobi da ke Tanzania
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi da lalata motocin yaƙin RSF
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030