Zanga-zanga ta ɓarke ranar Lahadi a faɗin ƙasar Iran bayan sanarwar da aka fitar cewa Amurka da Isra’ila sun kashe Jagoran Addini Ali Khamenei a hare-haren soji da suka kai ƙasar.
Lamarin ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin zaman zulumi kuma ya jawo kakkausan martani daga cikin ƙasar Iran.
Tun da farko gidan talbijin na Iran ya tabbatar da mutuwar Khamenei a hare-haren Amurka da Isra’ila, inda ya bayyana cewa Jagoran Addini na "Juyin-juya-halin Musulunci ya yi shahada.”
Kazalika gwamnatin ƙasar ta sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai.
Kafofin watsa labaran Iran sun ce masu zanga-zangar da ke riƙe da tutocin ƙasar Iran sun taru a cibiyoyin zanga-zanga a biranen ƙasar inda suke bayyana alhininsu.
A Tehran, ɗaruruwan mutane sun taru a Dandalin Inkilap, inda suke riƙe da tutocin ƙasar da fastocin Khamenei, inda suka riƙa Allah wadai da Amurka da Isra’ila.
A birnin Qom, ɗaruruwan mutane sun taru a Hubbaren Hazrat Masume domin yin tur da hare-haren.
A birnin Mashhad, masu zanga-zanga sun shimfiɗa baƙin ƙyalle a Hubbaren Imam Reza, ɗaya daga cikin wuraren da mabiya addini suke girmamawa a Iran, kuma an ga mutane da dama sun kuka a kusa da hubbaren.
An kashe iyalan Khamenei
Hukumomi a Iran sun tabbatar da cewa harin da aka kai da sanyin safiyar Asabar, ya yi ajalin Khamenei a yayin da yake ofishinsa a birnin Tehran.
Kafofin watsa labaran Iran sun musanta rahotannin da ke cewa yana gidan ƙarƙashin ƙasa a yayin da aka kashe shi, suna masu cewa “yana aiki tare da al’umma” a lokacin.
Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin.
Hare-haren sun yi sanadin fararen-hula da dama, inda ƙungiyar bayar da agaji ta Iranian Red Crescent ta ce adadin waɗanda aka kashe ya kai 201 sannan mutum 747 sun jikkata.















