Wasu ‘yanbindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 10 tare da banka wa gidan wani sarki wuta a wasu hare-hare da aka ce an tsara yin su a tare a jihar Kwara da ke tsakiyar Nijeriya, kamar yadda ‘yansanda suka bayyana a ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Adetoun Ejire-Adeyemi, ya ce “’yanta’adda” sun kai hare-hare lokaci guda kan fadar Sarkin garin Yashikira da kuma ofishin ‘yansanda na garin da misalin ƙarfe biyu na dare ranar Litinin.
Garin Yashikira yana da nisan kusan kilomita 190 daga babban birnin jihar, Ilorin.
“Yayin harin, an banka wa wani ɓangare na fadar sarki wuta, yayin da aka sace mutane 10 aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba,” in ji Ejire-Adeyemi.
Kungiyoyin masu ɗauke da makamai, waɗanda hukumomin tsaro da mazauna yankuna ke kira ‘yanbindiga, suna kai hare-hare kan ƙauyuka masu nisa, satar dukiya, ƙona gidaje da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, musamman a yankunan arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya.
Ejire-Adeyemi ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile harin da aka kai wa ofishin ‘yansanda.
Ya ƙara da cewa haɗaɗɗiyar tawagar jami’an tsaro na ci gaba da bincike a “dazuzzuka da maboyar masu laifi” domin ceto waɗanda aka sace.
A watannin baya-bayan nan, an samu ƙaruwar hare-haren tashin hankali a yankunan karkara da dama na jihar Kwara, inda ake danganta wasu daga cikinsu da ƙungiyoyin ta’addanci.
Aƙalla mutane 38 aka yi garkuwa da su daga wani coci a garin Eruku a watan Nuwamban 2025.
Mako guda bayan haka kuma, an sake sace wasu mutane 10 daga ƙauyen Isapa.
A watan Fabrairun 2026 kuwa, wasu ‘yanbindiga sun kashe akalla mutane 162 a ƙauyen Woro mai yawan al’ummar Musulmi.















