Matakin da Amurka ta ɗauka na korar jakadan Afirka ta Kudu “abin takaici ne,” kamar yadda ofishin shugaban kasar ya bayyana a ranar Asabar, yana mai kira ga "gyara diflomasiyya" tsakanin ƙasashen biyu.
"Fadar shugaban kasa ta kura da abin takaici na korar jakadan Afirka ta Kudu a Amurka, Mista Ebrahim Rasool," in ji sanarwar da Fadar Shugaban Afirka ta Kudu ta fitar.
Wannan na zuwa ne bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ya sanar da cewa, ba a maraba da jakadan na Afirka ta Kudu saboda shi "dan siyasa ne mai nuna ƙabilanci" wanda ya tsani Amurka da shugabanta.
Korar Rasool, wanda tsohon mai fafutukar yaƙi da wariyar launin fata ne ya ƙara haifar da rashin jituwa tsakanin Washington da Pretoria.
Trump a watan Fabrairu ya dakatar da kai agaji zuwa Afirka ta Kudu saboda wata doka a kasar da ya yi zargin cewa an ba da damar kwace filaye daga hannun manoma farar fata.
A makon da ya gabata, Trump ya kara dagula al'amura, bayan ya gayyaci farar fata mazauna Afirka ta Kudu da ke son barin ƙasar da su je Amurka za a ba su takardar zama ɗan ƙasa a cikin gaggawa.
Har ila yau gwamnatin Trump ta fusata kan ƙarar da Afirka ta Kudu ta kai Isra’ila a Kotun Duniya, inda Pretoria ke zargin Tel Aviv da aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza.













