| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
FIFA ta naɗa wa Nijeriya kwamitin mutum 5 don daidaita lamuran NFF, ciki har da Amokachi
A kwamitin akwai kuma tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles Daniel Amokachi.
FIFA ta naɗa wa Nijeriya kwamitin mutum 5 don daidaita lamuran NFF, ciki har da Amokachi
FIFA ta nada wa Nijeriya kwamitin mutum 5 don daidaita lamuran NFF, ciki har da Amokachi / Reuters (Wire)

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, ta sanar da cewa ta kafa wani kwamitin da zai daidaita lamuran Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF, watanni uku bayan shuwagabanninta sun ajiye aiki.

FIFA ta naɗa lauya Sampson Ebomhe, a matsayin shugaban kwamitin, wanda ya ƙunshi sanannen ɗanjarida, Godwin Enakhena, da wasu masana harkokin gudanarwa, Ms Amina Yerima da Dr Joe Abah.

A kwamitin akwai kuma tsohon kyaftin ɗin tawagar Super Eagles Daniel Amokachi.

A wata sanarwa daga Babban Jami’in kula da mambobin FIFA, “Waɗannan mutane da aka ambata a sama, mambobin kwamitin daidaita lamura za su karɓi aiki nan-take kuma za a musu tantancewa cancanta ƙarƙashin Kwamitin Bita na FIFA Review kamar yadda ƙa’idojin FIFA suka tanada.

Tabbatar da su a matsayin mambobi zai dogara kan sakamakon outcome binciken cancanta. Bugu da ƙari, babu ɗaya mambobin kwamitin daidaitawar da zai samu cancantar tsayawa takara a zaɓukan NFF da ke tafe ta kowane hali.

FIFA da bai wa kwamitin wa’adin zuwa ranar 31 ga Mayun 2027, sannan ta yanke masa jerin ayyukan da zai gudanar, baya ga gudanar da harkokin NFF.

Akwai bitar dokokin NFF da nufin ƙara wakilcin masu ruwa da tsaki, da tabbatar da kwamitin zartawar hukumar yana da daidaiton wakilin, tare da rage yawan mambobin kwamitin.