Wata kotun soji a ƙasar Guinea Bissau ta ba da umarni ranar Alhamis cewa a tsare jagoran ‘yanadawa a ƙasar Domingos Simoes Pereira a gida, bayan an sake yi masa tambayoyi game da zarge-zargen kitsa juyin mulki ga gwamnati, kamar yadda lauyansa ya bayyana .
An tsare Pereira, shugaban jam’iyyar PAIGC, a lokacin da sojoji suka yi wa Shugaba Umaro Sissoco Embalo juyin mulki ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 2025.
An sake shi a ƙarƙshin sharaɗin yi masa ɗaurin talala a watan Janairu, amma an zarge shi da hannu a yunƙurin juyin mulki biyu da aka yi a baya, ɗaya a shekarar 2023 ɗaya kuma a watan Oktoban shekarar 2025.
Jami’an tsaro da yawa ne suka kewaye kotun da Pereira ya gurfana a gabanta ranar Alhamis.
'Bai san kome game da shi ba'
Joao Paulo Indeque, ɗaya daga cikin lauyoyin Pereira, ya sanar da manema labarai cewa mutumin da yake karewa ya amsa duk tambayoyin alƙali.
"Domingos Simoes Pereira ba shi da hannu a ko wane yunƙurin zagon ƙasa ga gwamnatin da ke bisa tsarin mulki . Bai san kome game da shi ba, muna da tabbacin hakan," kamar yadda Indeque ya bayyana.
Janar Horta N'Tam ne ke jagorantar gwamnatin riƙon ƙwarya da ke mulki a Guinea Bissau a halin yanzu.









![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)



