An ji harbe-harbe da ƙarar fashewar wasu abubuwa a yankin Tahoua na Nijar
Wannan lamari da ya faru a yankin Tahoua yana zuwa ne ’yan makonni bayan wani hari da ƙungiyar Daesh ta kai babban filin jirgin saman ƙasar da ke birnin Yamai.
An ji ƙarar harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa masu ƙarfi a yankin Tahoua na Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi da tsakar dare, amma daga bisani lamura sun koma daidai, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.
Kimanin shekaru goma ke nan da kasar Nijar ke fama da tashe-tashen hankula daga ƙungiyoyin ta’adda masu alaƙa da Al-Qaeda da kuma Daesh.
Wannan lamari da ya faru a yankin Tahoua yana zuwa ne ’yan makonni bayan wani hari da kungiyar Daesh ta kai babban filin jirgin saman kasar da ke birnin Yamai.
“Mun ji ƙararrakin harbe-harbe masu ƙarfi sannan muka ji ƙarar fashewar wasu abubuwa da misalin karfe 3:00 na dare (wato karfe 2:00 GMT),” in ji wani mazaunin Tahoua kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mazaunin garin ya ƙara da cewa, maharan da ba a tantance ko su wane ne ba “sun zo ne a kan babura,” kuma an yi musayar wuta a hanyar filin jirgin saman birnin da kuma tsakiyar garin.
Sannan wani mazaunin garin ya shaida wa AFP cewa kafin fitowar alfijir “an daina jin ƙarar harbe-harbe, kuma kwanciyar hankali ta dawo.”
Har zuwa safiyar Litinin, babu wani bayani kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko suka jikkata sanadin al’amarin.
Idan za a tuna a makon da ya gabata an kashe wani jami’in kwastam da aƙalla fararen-hula uku a wani hari da aka kai wani shingen binciken ababen hawa kusa da iyakar Nijeriya a yankin na Tahoua.
Yankin na Tahoua a Nijar na ɗaya daga cikin wuraren da ’yan fashi da makami ke ɓuya, sannan kuma hanya ce da ake bi wajen fasa-ƙwaurin man fetur, miyagun ƙwayoyi, da kuma magungunan jabu.