| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200
Wani bayanin ma'aikatar lafiya ya ce an rubuta mutuwar mutane 204 a cikin larduna uku na kasar mai fadi a tsakiyar Afirka, daga cikin mutane 867 da ake zargi sun kamu cutar.
Adadin mutanen da Ebola ta kashe a Jamuhuriyar Kongo ya wuce 200
Jami'an lafiya a DRC sun ce aƙalla mutane 204 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola ya zuwa ranar 23 ga watan Mayu. / Reuters

Jami'ai a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun sabunta ƙididdigar mutanen da suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar Ebola zuwa 204 a cikin daren Asabar, 'yan sa'o'i bayan da Hukumar Red Cross ta ce masu aikin sa kai uku sun mutu a can, sannan kuma Uganda ta tabbatar da karin mutum uku da suka kamu da Ebola.

Wani bayanin ma'aikatar lafiya ya ce an rubuta mutuwar mutane 204 a cikin larduna uku na kasar mai fadi da ke tsakiyar Afirka, daga cikin mutane 867 da ake zargi sun kamu cutar. Kididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya ta ranar Jumma'a ta nuna adadin matattu 177 daga mutum 750 da ake zargin sun kamu da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana ɓarkewar cutar zazzabin zubar jini mai yaɗuwa wadda aka fi sani da Ebola a matsayin matsalar lafiyar gaggawa ta ƙasa da ƙasa.

Cutar a Uganda

A ranar Asabar, Hukumar Kiwon Lafiya ta Tarayyar Afirka ta yi gargaɗin cewa ƙarin ƙasashe a nahiyar na cikin haɗarin fuskantar cutar Ebola, baya ga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Uganda.

"Muna da ƙasashe 10 da ke cikin haɗari," in ji Jean Kaseya, shugaban Cibiyoyin Daƙile Cututtuka na Afirka (Africa CDC), yana lissafa: Angola, Burundi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Jamhuriyar Kongo, Ethiopia, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da Zambia.

Kaseya ya ce yawan tafiye-tafiye da rashin tsaro a yankin na taimakawa yaɗuwar cutar.

Sabbin masu ɗauke da cutar da aka tabbatar a Uganda a ranar Asabar yanzu sun kawo adadin wadanda aka tabbatar zuwa guda biyar a cikin ƙasar da ke gabashin Afirka tun lokacin da aka gano cutar a can da a Kongo a ranar 15 ga Mayu. Mutum guda ne a Uganda ya mutu.