Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da wata babbar masana'antar sarrafa lithium a Yammacin Afirka, a daidai lokacin da gwamantin ƙasar ke ƙara himma daga fitar da ma'adanai zuwa sarrafa su a cikin gida.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya ƙaddamar da masana'antar a Jihar Nasarawa a ranar Alhamis, yana mai cewa wurin na nuna ƙoƙarin ƙasar na ƙara daraja ga albarkatun ma'adinai masu yawa da ake da su a ƙasar, da ƙirƙirar ayyukan yi da kuma jawo hankalin masu zuba jari.
Masana'antar, wacce Kamfanin Avatar New Energy Materials ya gina, ana sa ran za ta sarrafa ma'adinan lithium zuwa kayayyaki masu daraja don amfani da su a cikin batirin motocin lantarki da sauran fasahar makamashi mai tsabta.
Da yake jawabi a wurin bikin buɗe wurin, Tinubu ya ce dole ne Nijeriya ta sauya daga fitar da kayayyaki ta gina masana'antu waɗanda ke iya sarrafa ma'adanai a cikin gida.
"Wannan ita ce hanyar ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa, masana'antu da wadatar ƙasa," in ji shugaban, yana mai ƙara da cewa sarrafa kayan cikin gida zai ƙarfafa matsayin Nijeriya a cikin kasashen da suka yi fice wajen samar da ma'adanai masu mahimmanci a duniya.
Aikin ya yi daidai da manufar gwamnati na ƙarfafa masu zuba jari gwiwa na su kafa wuraren sarrafa ma'adanai a cikin ƙasar maimakon fitar da su waje.
Nijeriya ƙasa ce wacce da arzikin ma’adanin lithium mai daraja, wanda ake amfani da shi a wajen haɗa batura masu caji da ake amfani da su ga motocin lantarki, wayoyin hannu da kuma tsarin adana makamashi da ake sabuntawa.
A 'yan shekarun nan bukatar lithium ya karu sosai a duniya, la’akari da yadda ƙasashe da dama ke koƙarin sauyawa zuwa makamashi mai tsafta.
Ministan Ci Gaban Ma'adanai a Nijeriya, Dele Alake ya ce sabon wurin na nuna wani muhimmin ci gaba a kudurin Nijeriya na zama jagora a fannin samar da ma'adanai.
Ya ce gwamnati tana aiwatar da gyare-gyare don inganta fannin hakar ma'adinai da kuma jawo hankalin masu zuba jari, tare da tabbatar da cewa al'ummomin yankunan da ake haƙo ma’adanan sun amfana.
Masu sharhi kan ayyukan masana'antu sun ce faɗaɗa ƙarfin sarrafa kayayyakin cikin gida zai iya taimaka wa Nijeriya ƙara daraja albarkatun ma'adinanta.
Sai dai, sun ce ci gaba da saka hannun jari a fannin ababen more rayuwa, da samar da wutar lantarki da hanyoyin sufuri suna da matukar mahimmanci ga ɓangaren don haɓaka shi zuwa gaba.
An kiyasin cewa Nijeriya na da ma'adinan lithium a jihohi da dama, ciki har da Nasarawa, Kogi, Kwara, Ekiti da Kaduna, wanda hakan ya sanya ƙasar a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe da ke da arzikin ma'adanai masu muhimmanci a duniya.










