Jam’iyyar adawa ta ADC a Nijeriya ta nemi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) sauya bayanan shugabanninta da sunan ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Ta kuma nemi kotun ta hana INEC sauya bayanan ’yan takararta na gwamna har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da ta shigar kan hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
A ranar Talata ne Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels.
Hukuncin Mai Shari’a Lifu na ranar 5 ga watan Nuwamba, wanda ya biyo bayan ƙarar da Nafiu Bala Gombe ya shigar, ya jefa shugabancin jam’iyyar da shirinta na tunkarar zaɓen 2027 cikin sabon ruɗanin shari’a da rashin tabbas.
Jam’iyyar ta ce ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin na ranar 5 ga watan Nuwamba, wanda ta bayyana a matsayin mai rauni. Ta kuma yi zargin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron batun takaddamar shugabancin jam’iyyar.
ADC ta kuma ce tana ƙalubalantar wani hukunci na farko da ya bai wa Bala Gombe damar gyara sammacin ƙarar da ya shigar, duk da cewa har zuwa lokacin ba a warware batun hurumin kotun na sauraron ƙarar ba.
Shaibu ya ce hujjoji 17 da jam’iyyar ta gabatar a ɗaukaka ƙarar sun haɗa da batun hurumin kotun na sauraron ƙarar, ikon Nafiu Bala Gombe na shigar da ƙarar, tantance sahihancin hujjar da ake takaddama a kanta, da kuma umarnin da kotun ta bayar kan jam’iyyar.
ADC ta ce bai wa INEC damar aiwatar da hukuncin kotun na ranar 5 ga watan Nuwamba kafin Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke hukunci kan batutuwan da ake takaddama a kansu na iya kawo cikas ga ɗaukaka ƙarar da ta shigar, tare da jefa takararta cikin rashin tabbas.
Jam’iyyar ta buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kare shugabancinta na yanzu da kuma bayanan ’yan takararta har zuwa lokacin da za a warware takaddamar shari’ar.























