Iran ta ce ‘a buɗe’ Mashigar Hormuz take, amma jiragen ruwa na tsoron wucewa
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa ba a rufe mashigar ba, amma “yanzu abubuwa sun sauya, ba yadda aka saba ba”
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Mashigar Hormuz a buɗe take, amma jiragen ruwa suna fargabar wucewa saboda yaƙin da Amurka da Isra’ila suke yi da Tehran.
“Ba a rufe Mashigar Hormuz take ba. Jiragen ruwa suna shakkar wucewa ne saboda kamfanonin inshora suna tsoron yaƙin son rai da kuka bijiro da shi — ba Iran ba,” in ji Abbas Araghchi a shafinsa na X a ranar Lahadi.
Ya ƙara da cewa, “Babu wani kamfanin inshora — kuma babu wani ɗan Iran — da zai firgita da ƙarin barazanar da kuke yi. Ku gwada girmamawa.”
“Yancin zirga-zirga a teku ba zai iya wanzuwa ba, ba tare da ’yancin yin ciniki ba. Ku girmama duka biyun — ko kuma ku rasa duka biyun.”
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar a shafin X, ta kuma ce “ba a rufe” Mashigar Hormuz ba.
Sai dai ta ƙara da cewa, jiragen ruwa “na ɓangarorin da suke yaƙarmu ba za su iya wucewa ta hanyar cikin lumana ba, kuma za a kawar da su daidai da tsarin shari’a da ya taso daga rikicin, sannan kuma da matakan da hukumomin Iran da abin ya shafa suka yanke.”
Rufe Mashigar
Tun farkon watan Maris, Iran ta rufe Mashigar Hormuz, wadda muhimmiyar hanyar jigilar man fetur ce da aƙalla take ɗaukar gangar mai kusan miliyan 20 a kowace rana, sannan kuma kusan kashi 20 cikin 100 na cinikin iskar gas (LNG) na duniya.
Rufe mashigar ya yi sanadiyyar tashin farashin jigilar kaya da inshora, ya sanya farashin ɗanyen mai yin sama, sannan ya haifar da matsalar tattalin arziki a duniya.
A ranar Asabar, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar “ruguza” tashoshin samar da wutar lantarki na Iran, ciki har da mafi girma, muddin Iran ba ta buɗe wannan mashigar mai muhimmanci ba nan da sa’o’i 48 ba.
Rikici a yankin ya tsananta tun bayan da hare-haren Amurka da Isra’ila suka fara kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, inda Tehran ta mayar da martani da jerin hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami da suka nufi Isra’ila da ƙasashen Larabawa da ke da sansanonin dakarun Amurka.