Rikicin da ya ƙara ta'azzara tsakanin Amurka, Isra'ila, da Iran ya kawo cikas ga daya daga cikin hanyoyin ruwa mafi cunkoso a duniya, wanda hakan ya tilasta wa manyan kamfanonin jigilar kaya sauya hanya inda suka bi da kewayawa ta fadin Afirka.
Kamfanonin jigilar kaya na duniya, ciki har da Maersk, Hapag-Lloyd da CMA CGM, sun dakatar da zirga-zirga a Mashigin Suez (Suez Canal) da Bab el-Mandeb bayan hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran da kuma ƙaruwar haɗarin tsaro a kusa da Mashigar Hormuz.
Mashigar Hormuz, wata ƙaramar hanyar ruwa ce tsakanin Iran da Oman, kuma tana daga cikin mahimman hanyoyi don jigilar mai, gas da kaya daga yankin Gulf.
"Sakamakon tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya bayan ƙarin rikicin soja, mun yanke shawarar dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Mashigar Suez da Maliya da Bab el-Mandeb na ɗan wani lokaci," in ji Maersk a cikin wata sanarwa.
A yadda aka saba, jiragen ruwa daga Asiya da Gabas ta Tsakiya zuwa Turai na wucewa ta Mashigar Hormuz — matattarar ruwa tsakanin Iran da Oman — kafin su ƙetare Tekun Larabawa su shiga Bahar Maliya ta Bab el-Mandeb, wanda ke tsakanin Yemen da Djibouti.
Daga nan jiragen suna bi arewa ta Mashigar Suez a Masar su shiga Bahar Rum a kan hanyar zuwa tashoshin Turai kamar na Italiya, Girka da Spain.
Lalacewar jiragen ruwa
Aƙalla tankokin mai guda uku sun samu lahani a bakin gabar Gulf, kuma ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgi ya mutu yayin da ramuwar gayya ta Iran ga hare-haren Amurka da Isra'ila ta sa jiragen suka fuskanci lahani, kamar yadda majiyoyin jigilar kaya da jami'ai suka shaida wa Reuters News Agency.
Hadarin ga jigilar kasuwanci ya ƙaru cikin awanni 24 da suka gabata, inda fiye da jiragen ruwa 200, ciki har da tankokin mai da na iskar gas suka dakata a kusa da Mashigar Hormuz da ruwan da ke kewaye suka daina tafiya, kamar yadda bayanan jigilar ruwa suka nuna a ranar Lahadi.
Manyan jiragen ruwa masu jigilar kwantenoni sun sauya hanyarsu ta hanyar yin kewaye ta Cape of Good Hope na Afirka ta Kudu, wato ƙarshen kudu da Cape Peninsula.
Har yanzu ba a gano wanda ya harba jiragen yaƙi marasa matuƙa da suka kai hari kan jiragen ruwa har suka lalata su ba a ranar Lahadi.
Donald Trump a daidai lokacin ya ce Amurka ta halaka jiragen ruwan rundunar sojin ruwa na Iran guda tara kuma ta raunana hedkwatar rundunar ruwa ta Iran.
Daruruwan jirage sun tsaya cak sun dakata da tafiya.
Tun da an ɗauki wannan hanya a matsayin marar aminci, dole jiragen su nufi kudu ta fadin Tekun Indiya, su bi gabar gabashin Afirka, su kewaya Cape of Good Hope sannan su nufi arewa ta cikin Tekun Atlantika zuwa Turai.
Wannan kewaye yana ƙara dubban kilomita kuma na iya tsawaita tafiya har zuwa makonni biyu.













