NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Kwamitin Shura kan harkokin addini da zamantakewa
Majalisar ta ƙunshi mambobi 67 waɗanda aka zaɓo daga faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da Kwamitin Shura kan harkokin addini da zamantakewa
Majalisar ta ƙunshi mambobi 67 waɗanda aka zaɓo daga faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano. / Others
9 Satumba 2025

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da Majalisar Shura, a matsayin wani sabon kwamiti don jagoranta da ba da shawarwari kan al’amuran da suka shafi addini da zamantakewa da ke shafar ‘yan jihar.

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamarwar a gidan gwamnati, Gwamnan ya bayyana majalisar a matsayin wani muhimmin ginshiki na kokarin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, gaskiya, da haɗin kai a harkokin mulki.

A cewarsa, Majalisar Shura za ta taka muhimmiyar rawa wajen bayar da shawarwari kan harkokin addini da na jama’a tare da tabbatar da cewa ana jin muryoyin ‘yan kasa wajen yanke shawara.

"Manufar wannan gwamnati ita ce tabbatar da cewa mutane sun shiga cikin harkokin mulki. Muna son 'yan jiharmu su ba da gudunmawar ra'ayoyinsu da shawarwari don ci gaban jihar baki daya."

Ya kara da cewa majalisar za ta taimaka wajen dinke barakar da ke tsakanin shugabanni da masu mulki ta hanyar samar da gaskiya da sanya ra’ayoyi daban-daban cikin manufofin gwamnati.

Tun da farko Sakataren Majalisar Shurah Alhaji Shehu Wada Sagagi ya sanar da nadin Wazirin Kano Sheikh Sa’ad Shehu Gidado a matsayin Shugaban Majalisar inda Farfesa Sani Zaharaddeen ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar.

Mambobin majalisar sun hada da fitattun malaman addinin Musulunci da ƙwararru da shugabannin 'yan kasuwa, da wakilan al'umma.

Jami’ai sun ce da an tsara manyan ‘yan majalisar ne domin bai wa kwamitin halacci da kuma tabbatar da cewa shawarwarin da ya bayar sun yi daidai da muradun ‘yan kasa baki daya.