Shugaban Majalisar Mulkin Rikon Kwarya ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya bukaci kasashe masu arziki su ninka tallafin kudaden da suke bai wa kasashe masu tasowa domin taimaka musu wajen shawo kan illolin sauyin yanayi.
Al-Burhan ya kuma bukaci a samar da hanyoyin samun tallafin cikin sauri da adalci, ba tare da sanya siyasa cikin tsarin yanke shawarar raba tallafin ba.
Da yake jawabi a ranar Laraba, a zaman farko na taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na COP31 da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a birnin Antalya na Turkiyya, Al-Burhan ya ce dole ne alkawuran tallafin sauyin yanayi su koma kudaden da kasashe masu tasowa za su iya samu cikin sauri da sauki da kuma adalci.
Ya bukaci kasashe da suka ci gaba da su kara kokarinsu tare da ninka tallafin kudaden da ake warewa domin taimakawa kasashe su yaki illolin sauyin yanayi.
Ya kuma yi kira ga gwamnatoci da su mayar da matakan da aka dauka a matsayin hanyoyin bunkasa ci gaba, da zaman lafiya, da tsaro da kuma adalci.
Al-Burhan ya bayyana cewa Sudan na fuskantar barazanar karuwar fari, da ambaliyar ruwa, da kwararowar hamada, da lalacewar filaye da kuma karancin ruwa.
Kazalika ya kara da cewa, raguwar ayyukan noma da kiwon dabbobi na barazana ga samar da abinci da hanyoyin samun abin dogaro ga al'ummar kasar.
Ba da fifiko ga kasashen da suka fi fuskantar barazana
‘‘Yanayin na musamman da Sudan take ciki ya kara tsananta wadannan matsaloli, musamman ta fuskar lalacewar ababen more rayuwa, da ayyukan hidimar jama'a da cibiyoyin gwamnati, da kuma karfin al'umma wajen tinkarar illolin sauyin yanayi,’’ a cewar Al-Burhan.
Ya bukaci a ci gaba da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa adalci da ka'idar cewa dukkan kasashe suna da nauyin yaki da sauyin yanayi, sai dai gwargwadon gudummawarsu da karfinsu ya bambanta.
Haka kuma Al-Burhan ya bukaci kasashe su yi la'akari da yanayi da bukatun kasashe masu tasowa, musamman kasashe mafi karancin ci gaba da wadanda rikice-rikice suka shafa.
Idan za a tuna, tun a watan Afrilun 2023 yaki tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun rundunar kai daukin gaggawa ta RSF ya barke.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, tare da takaita samun ruwan sha mai tsafta, da kiwon lafiya da matsugunai a wasu sassan kasar.



















