Hukumar leƙen asirin Somalia ta kashe masu haɗa bama-baman Al Shabab

An kuma lalata kayayyakin haɗa bama-bamai a tagwayen samamen da suka kashe 'yanta'addan Al Shabab 28.

By
TSOHON HOTO: Somalia tana samun nasara kan ƙungiyar 'yanta'addan al Shabab . / AA / AA

Hukumar leƙen asiri da tsaron Somalia (NISA) ta bayyana ranar Talata cewa ta ƙaddamar da wasu tagwayen samame da suka kashe ‘yanta’addan Al Shabab 28.

Samamen da suka kai tare da abokan aiki na ƙetare da ke taimaka wa gwamnatin tarayyar ƙasar sun faru ne a kudancin lardunan Lower Shabelle da Middle Shabelle.

Ɗaya daga cikin samamen da aka kai a yankin Kunyo Barrow, a lardin Lower Shabelle, ya mayar da hankali ne kan kayayyakin Al Shabab na ɓoye, waɗanda ƙungiyar ke amfani da su wajen haɗa bam da kuma gyara makamai.

An kashe ‘yanta’adda bakwai, ciki har da injiniyoyi masu haɗa bama-bamai na ƙungiyar, yayin da harin sama na biyu a lardin Middle Shabelle ya kashe ‘yanta’adda 21, kamar yadda NISA ta bayyana a wata sanarwa.

“Samamen ya lalata kayayyakin fasaha da kayayyakin da aka tara a wuraren da kuma motoci biyu da ake haɗawa da abubuwan fashewa,” in ji sanarwar.

Al Shabab ta ƙaddajar da hare-haren ta’addanci kan gwamnatin Somalia na tsawon shekaru 16, inda a mafi yawan lokuta ta kan kai hari kan dakarun tsaro da jami’ia da fararen-hula.

Tun watan Yulin da ya gabata, sojin Somalia da tallafin dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar tarayyar Afirka ko kuma AUSSOM, da wasu abokan aiki na ƙasashen waje sun ƙarfafa ayyukansu kan ƙungiyar inda suke mara wa gwamantin tarayyar ƙasar baya.

A watan Disamba ne Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta sabunta wa’adin aikin AUSSOM na ƙarin shekara ɗaya da wani ƙuduri da ya matsa ƙarshen aikinsa zuwa ranar 31 ga watan Disamba.​​​​​​​