Wani hari na makami mai linzami da Iran ta kai sansanin sojin sama na Yarima Sultan a ƙasar Saudiyya ya jikkata sojojin Amurka aƙalla 12, cikinsu har da biyu da suka samu munanan raunuka, sannan ya lalata jiragen da ke zuba mai ga jiragen yaƙi dama, a cewar kafofin watsa labaran Amurka.
Jaridar Wall Street Journal ta ambato wasu jami’ai suna cewa baya ga makami mai linzami, an kai harin da wasu jirage marasa matuƙa.
Iran ta kai harin ne a yayin da yaƙin yake ci gaba da yin ƙamari, inda Rundunar Sojin Amurka ta bayyana cewa sojojinta fiye da 300 sun jikkata a makonni huɗu da suka yi suna gumurzu da Iran.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce yaƙin zai ci gaba zuwa ƙarin “makonni biyu zuwa huɗu,” kuma hana Iran ƙaƙaba haraji kan jiragen ruwa da ke bi ta Mashigar Hormuz shi ne zai kasance babban ƙalubalen da za su fuskanta bayan kammala yaƙin.
Ya bayyana matakin na Iran a matsayin wanda “bai halasta ba” kuma “mai matuƙar hatsari ga duniya.”
A gefe ɗaya, Isra’ila ta kai jerin hare-hare a Iran.
Farashin gangar ɗanyen mai ya tashi fiye da $100 sakamakon wannan sabon farmaki, yayin da hannayen-jarin Amurka suka faɗi bayan Shugaba Donald Trump ya dakatar da kai hari kan tashoshin makamashin Iran.
A Yemen, ‘yan Houthi sun nuna cewa za su iya faɗaɗa yaƙin. Ƙungiyar, wadda ke iko da yawancin ƙasar, ta ce “sun shirya domin shiga yaƙin kai tsaye” idan ƙarin ƙasashe suka shiga yaƙi da Tehran, ko kuma idan Amurka ko Isra’ila suka yi amfani da Bahar Maliya wajen ayyukan soja.
A ranar Juma’a, Iran ta gargadi jiragen ruwa uku da kada su bi ta Mashigin Hormuz, kwana guda bayan Donald Trump ya tsawaita wa’adin Amurka ga Tehran domin sake buɗe hanyar.
A martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila, Iran na iko da mashigin, wata muhimmiyar hanya ga zirga-zirgar mai da iskar gas na duniya, abin da ke tayar da hankalin kasuwanni a faɗin duniya.
Iran ta mayar da martani ga hare-haren Amurka da Isra’ila a kan yankinta da jerin hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami da suka nufi Isra’ila, Jordan, Iraq da ƙasashen Tekun Fasha da ke karɓar baƙuncin sojin Amurka, lamarin da ya jawo asarar rayuka da lalacewar ababen more rayuwa.






