Kamfanin Apple ya sanar da samun matsalar katsewar ayyuka a sassa daban-daban na tsarinsa, lamarin da ya shafi manyan shafukan intanet kusan 200 kana ya ƙara yawan tsaiko na fasaha da ya kawo cikas ga ayyuka a Amurka da sassan duniya.
A cewar shafin Apple da ke bayyana halin da tsarin ayyukansa ke ciki, an fuskanci jinkirin buɗe Asusun iCloud a ranar 17 ga watan Nuwanba.
Haka kuma, an samu katsewar sayen kayan AppleCare ta na'urorin kamfanin na wani ɗan lokaci, yayin da wasu masu amfani da Apple Business da Apple School Manager da kuma Schoolwork su ma suka fuskanci tsaiko.
Matsalolin sun zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin wani harin kutse na intanet da aka kai kan shafukan intanet na manyan kamfanoni da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai BBC, da CNN, da Zoom, da HSBC UAE, da Air France-KLM, da IKEA, da Salesforce da kuma GitLab.
A ranar Talata, kamfanin Google ya ce bai gano wata hujjoji da ke nuna cewa an samu katsewar ayyukan Gmail a faɗin duniya ba, duk da cewa dubban masu amfani da shafin sun bayar da rahoton fuskantar tsaiko yayin shiga asusunsu ko wajen duba saƙonnin imel.
"A halin yanzu, ba mu samu wata hujja da ke nuna cewa an samu katsewar ayyukan Gmail a faɗin duniya ba. Ƙungiyoyinmu na sanya ido sosai kan yanayin ayyukanmu, ko da yake ana iya samun sabbin bayanai kan halin da suke ciki a kowane lokaci ta shafin Google Workspace Status Dashboard," a cewar wani mai magana da yawun Google.
Sanarwar ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafe fiye da 2,800 da shafin Downdetector, mai bibiyar matsalolin ayyukan intanet ya samu kan matsalolin Gmail zuwa ƙarfe 12 na rana a agogon Gabashin Amurka (1700 GMT).
Vance ya buƙaci a kasance cikin shirin ko-ta-kwana
Kazalika lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Donald Trump ke fuskantar tambayoyi kan irin ƙarfi da tsarin fasahar sadarwar Amurka ke da shi na jure wa manyan matsaloli.
Da yake magana da Fox News a ranar Litinin, Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce gwamnatin ba ta hasashen samun wata babbar matsala, amma tana cikin shirin ko-ta-kwana don tunkarar duk wani mummunan yanayi.
"Ba mu ga wata babbar matsala da ke tafe ba, amma dole ne a kasance cikin shirin tunkarar duk wani mummunan yanayi," in ji Vance.
Ya ce manufar gwamnatin ita ce "tabbatar da cewa mun hana faruwar mummunan yanayi, tare da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana."
Kalamansa sun biyo bayan jerin matsalolin da suka shafi fannin sufurin jiragen sama, da harkokin banki, da hanyoyin sadarwar hukumomin gwamnati da kuma manyan ayyukan Microsoft da kamfanoni ke amfani da su.
Tsaiko ga kamfanonin jiragen sama da bankuna
Kamfanin Microsoft ya fuskanci babbar matsalar katsewar ayyuka tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Nuwamba, lamarin da ya shafi Outlook, da Teams da sauran ayyukan Microsoft 365 a faɗin duniya.
Kamfanin ya danganta tsaikon da wata matsalar kutsen fasahar manhaja da ba a gano ta ba a watan Yuli. Ya ce lamarin ta ta’azzara ne sakamakon ƙaruwar hanyoyin sadarwa da raguwar ƙarfin rumbun bayanansa.
A ranar 13 ga watan Nuwamba, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka (FAA) ta ba da umarnin dakatar da tashin jiragen sama a faɗin ƙasar bayan da hanyar sadarwarta ta fuskanci tsaiko yayin aikin sabunta layukan sadarwa na faiba.
Matsalar ta ɗauki tsawon sa'o'i da dama, tare da haddasa soke dubban tashin jiragen sama.
Haka kuma an sake samun wata matsala a ranar Litinin, bayan da kamfanin jiragen sama na United Airlines ya sanar da matsalar fasaha da ta shafi tsarin da ma'aikatan jiragensa ke amfani da shi, ciki har da bayanan nauyin jiragen sama.
Matsalar ta ɗauki tsakanin mintuna 30 zuwa 90 kafin a shawo kanta, inda ta haddasa jinkirin tashin jiragen kafin a dawo da ayyukan yadda ya kamata.
Kamfanin United Airlines ya ce babu wata alama da ke nuna cewa matsalar na da alaka da harin kutse ta yanar gizo.
Manyan bankunan Amurka ma sun fuskanci matsalolin ayyuka a ranar 16 ga watan Nuwamba.
Bankin Chase ya danganta matsalolin ayyukansa na intanet da wata matsala ta fasahar software, wadda ta kuma shafi wasu hada-hadar kudi da ke da alaka da wasu cibiyoyin kudi.
Bankin ya ce lamarin ba shi da alaka da harin kutse ta yanar gizo, kuma ba ya nuna cewa an samu matsala a dukkan tsarin hada-hadar kudi.
Matsalar ta shafi hanyoyin sadarwa na leken asirin Amurka
Rahotanni sun ce hanyar sadarwar sirri da Hukumar Tsaron Kasa ta Amurka (NSA) ke amfani da ita wajen sadarwa, wadda aka fi sani da NSANet, ta samu tangarda na dan wani lokaci a ranar 17 ga watan Nuwamba.
Wani jami'in Amurka ya danganta matsalar da aikin gyaran tsarin sadarwa da ake yi, ko da take ya ce , an ci gaba da gdanar da muhimman ayyukan hukumar.
Jami'an sun ce babu wata hujja da ke nuna cewa an kai harin kutse ta yanar gizo.
A wani rahoto na daban, kamfanin sa ido kan barazanar yanar gizo ta Google (Google's Threat Intelligence Group) ya yi gargadi a ranar Litinin cewa masu kutse suna kara amfani da na'urorin fasahar (AI) masu iya gudanar da ayyuka da kansu wajen kai hare-haren yanar gizo.
Kamfanin ya bayyana barazanar karuwar amfani da tsarin AI da ke iya gudanar da ayyuka ba tare da bukatar sa hannun dan Adam a kowane mataki ba a cikin rahotonsa mai taken "Agentic Threat Activity Crosses a Significant Threshold."























