| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Ranar Laraba ne shugaban ofishin ƙasa na WAEC a Nijeriya, Dr Amos Dangut ya bayyana hakan lokacin jawabinsa yayin sakin sakamakon jarrabawa a Lagos.
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Riƙewar na zuwa ne bisa zargin maguɗin jarrabawa. Sai dai adadin ya nuna raguwa daga kashi 9.7 cikin ɗari da aka gani a 2025.

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma, WAEC ta riƙe sakamakon masu jarrabawa 167,486, wanda ke wakiltar kashi 8.59 cikin ɗari na waɗanda suka zauna jarrabawar kammala babbar sakandare ta Yammacin Afirka ta 2026, wadda aka yi da kwamfuta.

Riƙewar na zuwa ne bisa zargin maguɗin jarrabawa.

Sai dai adadin ya nuna raguwa daga kashi 9.7 cikin ɗari da aka gani a 2025.

Ranar Laraba ne shugaban ofishin ƙasa na WAEC a Nijeriya, Dr Amos Dangut ya bayyana hakan lokacin jawabinsa yayin sakin sakamakon jarrabawa a Lagos.

Dr Dangut ya ce hukumar ta riƙe sakamakon waɗanda abin ya shafa ne saboda mabambantan dalilai, ciki har da ƙaruwar amfani da wayar hannu a ɗakunan jarrabawa duk da haramcin da ke akwai sannan da shirya maguɗi a tare, a wasu makarantu.

Masu AlakaTRT Afrika - Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane

Ya ƙara da cewa an kama wasu masu sa ido da masu kula da jarrabawa da aka samu suna taimaka wa ɗalibai wajen yin maguɗin jarrabawa, kuma za su fuskanci hukunci ta hannun ma'aikatun ilimi na jihohin da abin ya shafa.

Jimillar ɗalibai 1,959,668 daga makarantu 24,207 ne suka yi rajistar jarabawar a Nijeriya, Jamhuriyar Benin, Côte d’Ivoire da Equatorial Guinea, yayin da ɗalibai 1,950,726 suka zauna domin rubuta jarabawar.

Daga cikinsu, ɗalibai 1,200,514 (kashi 61.54 cikin 100) sun samu maki na Credit ko sama da haka a aƙalla darussa biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.

Haka kuma, ɗalibai 1,687,378 (kashi 86.50 cikin 100) sun samu Credit ko sama da haka a aƙalla darussa biyar, ko da kuwa sun haɗa da Ingilishi da Lissafi ko kuma ba su haɗa da su ba.

Rumbun Labarai
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Gwamnati ta ba jami’o’i da kwalejojin Nijeriya umarnin korar ɗalibai da ke da alaka da satar mutane
'Yansandan Nijeriya sun kama mutum 48 a samamen da suka kai maɓoyar masu laifi a Zamfara
An saki alƙalin da aka yi garkuwa da shi a jihar Kebbin Nijeriya
Dakarun Nijeriya sun daƙile harin daren 'yanta'adda kan sansanin soji
'Yanbindiga sun kashe mutum 12, sun yi garkuwa da mata da yara a wani ƙauye Sokoto a Nijeriya
Nijeriya ta tura sojoji 86 domin aikin wanzar da zaman lafiya a Guinea-Bissau
Sojojin Nijeriya sun daƙile yunƙurin 'yanta'adda na garkuwa  da mutane 31 a Borno
Remi Tinubu ta nemi Saudiyya ta tallafa wa ilimin almajirai a Nijeriya
Nijeriya ta lalata makamai guda 2,819 da ta kama a matakin dakile rashin tsaro
'Yansandan InterPol sun tasa ƙeyar ɗan China daga Nijeriya kan safarar namun daji
Nijeriya na da attajirai 7,200 masu arzikin dala miliyan 1 duk da raguwar kuɗi - Rahoto
'Yanbindiga sun kashe Kanar na sojin Nijeriya bayan ya ƙi amincewa su yi garkuwa da shi
Aƙalla mutane 14 ne suka mutu a wani hari da aka kai a jihar Benue ta Nijeriya, in ji jami’an yankin
'Yanta'adda sun kashe aƙalla mutum 30 a wani ƙauye a Kaduna ta Nijeriya
Ana fargabar ɗalibai sun maƙale bayan da gini mai ɗakuna 90 ya rufta da su
Rundunar Sojin Nijeriya ta kama jami'in da ake zargi da sayar wa 'yanta'adda kayan soji
Jami'in da ke kula da harkokin kuɗin ISWAP ya miƙa wuya —Rundunar Sojin Nijeriya
INEC za ta rufe rijistar masu zaɓe ranar Lahadi, 'yan adawa na neman a tsawaita lokacin rijistar
Sojojin Nijeriya sun ce suna ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara