"Lamarin da ya soma da hare-haren Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran, sannan ita ma Iran ta kai hare-hare ƙasashe uku, yana barazana ga makomar tsaron yankinmu da kuma duniya baki ɗaya," in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.
Aa wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta yi kira ga duka ɓangarorin su tsagaita wuta nan-take.
"Muna matuƙar nuna damuwa game da duk wasu matakai na karya dokokin ƙasashen duniya tare da yin barazana ga rayukan fararen-hula da ba su da laifi, kuma mun yi tir da tsokanar faɗa da za ta iya ta’azzara rikicin," a cewar sanarwar.
"Muna jaddada cewa lamuran da suka shafi yankinmu ya kamata a magance su ta hanyar zaman lafiya. A shirye Turkiyya take ta bayar da dukkan goyon bayan da ya dace wajen tattaunawar zaman lafiya. Tsaron lafiyar ‘yan ƙasarmu a ƙasashen da lamarin ke faruwa shi ne babban muradinmu, kuma muna ɗaukar dukkan matakai domin tabbatar da hakan," in ji ma’aikatar harkokin wajen.
Yunƙurin diflomasiyya na Hakan Fidan
Sanarwar na zuwa ne awanni bayan Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi magana ta wayar tarho da takwarorin aikinsa na Iran, Iraƙi, Saudiyya, Masar da Indonesia bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai Iran.
A cewar wasu majiyoyi daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, Fidan ya yi magana ta wayar tarho daban-daban da Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi, Ministan Harkokin Wajen Iraƙi Fuad Hussein, Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty, da Ministan Harkokin Wajen Indonesia Sugiono.
Yayin tattaunawar, manyan jami’an diflomasiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin da kuma matakan da suka kamata a ɗauka domin kawo ƙarshen rikicin.
Isra’ila da Amurka sun ƙaddamar da hare-hare a Iran da sanyin safiyar Asabar, suna masu zargin cewa “gwamnatin Iran” tana yi musu barazana.

















