| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Shugabannin duniya za su hallara a Turkiyya domin taron diflomasiyya na Antalya karo na 5
Fiye da shugabannin ƙasashe 20 da ministocin harkokin waje 50 ne za su halarci Taron Diflomasiyya na Antalya na shekarar 2026 (ADF2026) domin tattauna ƙalubalen siyasa, tattalin arziki, da na shiyyoyi.
Shugabannin duniya za su hallara a Turkiyya domin taron diflomasiyya na Antalya karo na 5
[TsohTaron Antalya Diplomacy Forum 2026 zai gabatar da tattaunawa 40 inda za a yi tsokaci kan batutuwan siyasa da na tattalin arzikin duniya
12 Afrilu 2026

A wannan watan na Afrilu, birnin Antalya na ƙasar Turkiyya zai sake zama cibiyar diflomasiyyar duniya, yayin da shugabannin duniya, ministoci, da manyan jami’ai za su taru don ɗaya daga cikin manyan tarukan ƙasa da ƙasa da aka saba yi.

Taron na bana, wanda zai gudana ƙarƙashin taken “Tsara Taswirar Gobe, Magance Halin Rashin Tabbas”, zai haɗa kan shugabanni domin tattauna yanayin rashin tabbas a duniya da kuma tsara makomar diflomasiyyar ƙasa da ƙasa.

Za a gudanar da taron diflomasiyya na Antalya karo na biyar ne daga ranar 17 zuwa 19 ga watan Afrilu.

Tun lokacin da aka ƙaddamar da shi a shekarar 2021, taron ya ci gaba da haɓaka har ya zama babban dandali na tattaunawa, haɗin gwiwa, da tuntuɓar juna a matakin ƙoli a duniya.

Ana sa ran taron na bana zai karɓi baƙuncin wakilai daga ƙasashe fiye da 150, ciki har da shugabannin ƙasashe, ministoci, da manyan jami’ai daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

A cewar wasu majiyoyi daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, fiye da shugabannin ƙasashe 20 ne ake sa ran za su halarci taron. Akwai mataimakan shugabannin ƙasa 15. Fiye da ministocin harkokin waje 50 za su hallara.

Gaba ɗaya, taron zai haɗa manyan mahalarta fiye da 460, ciki har da wakilai kusan 75 daga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, tare da baƙi kusan 5,000.

Wakilci Daga Sassan Duniya

Taron na ADF26 zai samu wakilci mai faɗi daga sassan duniya, inda kusan rabin shugabannin ƙasashen da za su halarta suka fito daga nahiyoyin Afirka da Turai.

Daga cikin ministocin harkokin waje, kashi 40 sun fito ne daga Afirka, kashi 35 daga Turai da kashi 22 daga Asiya.

Tattaunawa Kan Batutuwan Da Suka Shafi Duniya

Taron zai ƙunshi zaman tattaunawa fiye da 40 da kuma taron shugabanni, waɗanda za su mayar da hankali kan sauye-sauyen duniya, rashin tabbas, da canjin yanayin harkokin shiyyoyi. Haka kuma, za a tattauna manyan ƙalubale na siyasa, tattalin arziki, muhalli, da fasaha da ke tsara yanayin sabon tsarin duniya.

Wasu daga cikin tarukan da da a yi za su mayar da hankali kan batutuwa kamar: halin da ake ciki a Gaza da batun Kungiyar Ƙasashen Turkic, da kuma taron kasashe huɗu da zai haɗa Turkiyya, Pakistan, Saudiyya da kuma Masar.