Wasu matan Afirka na fama cutar sepsis bayan haihuwa wadda ake iya rigakafinta
Shirin WHO na APT-Sepsis a Malawi da Uganda ya nuna cewa mace-macen masu ciki sakamakon kamu wa da cututtuka da za a iya rigakafinsu na iya raguwa da kusan kashi ɗaya bisa uku idan asibitoci suka aiwatar da ka'idojin tsafta da matakan yin magani.
Goma sha ɗaya cikin 1,000 na kowace mace da ta yi haihuwar fari a duniya na kamuwa da cututtukan bayan haihuwa waɗanda ka iya janyo rashin aiki a gabobin jiki ko ma mutuwa.
Babban abin da ya fi tayar da hankali a cikin bayanan da aka fitar a Nazarin Cutar Sepsis ta Duniya ta 2020 (GLOSS) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), shi ne cewa duk waɗannan mace-macen ana iya hana su afkuwa.
Kwanaki kadan bayan ta haifi ɗanta a wani asibiti a Uganda, Grace Nalwoga ta kusan faɗa wa cikin mummunan yanayin kamuwa da cutar bayan haihuwa ta sepsis..
Abin da ya faro a matsayin murmurewa ta al'ada daga haihuwa ya koma matsala cikin sauri yayin da Grace ta kamu da zazzabi mai ƙarfi har ta ji rayuwa ta fara barin ta.
"Zafi da radadi a cikina sun yi yawa," Grace ta shaida wa TRT Afrika. "Na yi rauni a kowace sa’a. Ina tuna kallon jaririna kuma ina jin tsoron kada in mutu ba tare da shaida ganin ya girma ba."
Grace ta kamu da wani mummunan ciwo bayan haihuwa wanda ya kai ta ga kamu wa da cutar sepsis, wata cuta mai barazana ga rayuwa inda martanin da jiki ke mayarwa ga cutar yake lalata kwayoyin halitta da gabobin jiki.
Tana ɗaya daga cikin mata marasa adadi waɗanda cutar sepsis ta maye gurbin farin cikin haihuwar da suka yi, cutar da ke janyo mutuwar iyaye mata bayan haihuwa a Afirka da sauran sassan duniya da dama.
Da yawa daga cikin waɗannan sabbin iyaye mata suna mutuwa saboda asibitoci ba sa bin ƙa'idodin tsabta da matakan amfani da magani.
WHO ta bayyana tsaftar hannu a koyaushe, gano cutar da wuri da kuma magani a kan lokaci a matsayin manyan abubuwan da ke haifar da hana sepsis kama iyaye sabbin haihuwa.
Matakan kubutar da rayuka
A Malawi, fama da Alice Kambalame ta yi da wata cuta bayan tiyata ya faro ne bayan nakuda mai tsawo wadda ta kai ga haihuwarta ta hanyar tiyatar haihuwa.
"Bayan tiyatar, na san akwai wani abu da ba daidai ba," in ji Alice ga TRT Afrika. "Raunin ya yi ja kuma yana da radadi, kuma na ji jiri da rikicewa. Likitoci da ma'aikatan jinya sun yi aiki da sauri.
“Sun gaya mini cewa ina da wata cuta kuma nan da suka fara ba ni magani. Na yi imanin cewa gaggawarsu ce ta tsirar da rayuwata.”
Bambancin da ke tsakanin 'yar tsallake rijiya da baya da Grace ta yi da hanzarin kulawa da Alice ta samu ne abinda wani sabon bincike ya tabbatar yanzu.
Binciken da aka buga a mujallar ‘New England Journal of Medicine’ ta WHO, Shirin Musamman na Haihuwar Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya (HRP) da Jami'ar Liverpool sun nuna cewa tsarin rigakafi da kulawa da kamuwa da cutar zai iya rage kamuwa da cutar mai tsanani da mace-mace a tsakanin mata da sama da kashi 30%.
Gwajin, wanda aka gudanar a asibitoci 59 a Malawi da Uganda kuma a kan mata sama da 431,000, ya haifar da aiwatar da shirin Rigakafi da Maganin Cutar Sepsi da ake kamu wa da ita yayin ko bayan Haihuwa (APT-Sepsis).
Shirin yana tallafawa ma'aikatan kiwon lafiya wajen cike gibin da ke akwai a kulawa ta hanyar ƙarfafa "lokaci biyar na tsaftace hannu", amfani da ingantattun ka’idojin rigakafin kamu wa da cutar, da kuma amfani da "FAST-M treatment fast-M" na amfni da ruwan magani, ntibiotics da snaya idanu..
Matakai masu tasiri
Asibitocin da ke amfani da matakan APT-Sepsis sun sami raguwar mace-macen mata masu dauke da cutar da kuma mummunar rashin lafiya da kashi 32%.
Sun kuma bayar da rahoton samun ci gaba mai muhimmanci wajen bin ƙa'idojin tsaftace hannu, amfani da maganin rigakafi yayin tiyatar CS, da kuma sa ido akai-akai kan manyan alamun kamuwa da cututtukan da wuri.
"Shirin APT-Sepsis shaida ce ta abin da za a iya cim mawa lokacin da kimiyya, manufofi da kulawar kan gaba suka haɗu," in ji Dr Jeremy Farrar, mataimakin babban darakta a WHO.
"Rage kamu wa da cutar da mace-mace a tsakanin mata masu juna biyu da sama da kashi 30% ba wai kawai nasara ce ta asibiti ba; kira ne ga tsarin kiwon lafiya na duniya don bayar da fifiko ga rigakafin kamu wa da cutar sepsis ta hanyar kula da mata masu juna biyu.
Dole ne mu tabbatar da cewa an haɓaka waɗannan ayyukan ceton ran kuma an ci gaba aiki da su a duk wurare."
Kananan nasarori
Ga iyaye mata irin su Alice, a ƙarshe akwai tsarin da aka tsara don hana kamu wa da cututtukan bayan haihuwa da kuma tabbatar da kulawa mai inganci idan sepsis ta afku.
Nasarar da wannan tsarin ya samu a Malawi da Uganda ya sa WHO da abokan hulɗarta sun faɗaɗa shi a cikin tsarin kiwon lafiya na ƙasa a duk faɗin duniya.
Yayin da Grace ke kallon ɗanta yana wasa, tana jin daɗin samun damar bayar da labarin abin da ta fuskanta don kada wasu su yi hakan.
"Godiya ga Allah, na tsira ta yadda zan iya bayar da labarina," Grace ta shaida wa TRT Afrika. "Lokacin da na ga ɗana yana farin ciki da wasa, ina tunanin duk sauran iwaye mata waɗanda za su ga 'ya'yansu suna girma saboda wannan sabon tsarin kulawa. Wannan nasara ce mai kyau."