Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara
Shugaban hukumar ta MDD ya ce an sanya hannu kan yarjejeniya da gwamnatin Turkiyya don bude ofishinsu a Ankara.
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta gana da Philippe Lazzarini, shugaban hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya kan 'Yan Gudun Hijira Falasɗinawa (UNRWA), a Ankara ranar Alhamis, yayin da shugaban hukumar ya sanar da shirin buɗe ofishin UNRWA a babban birnin Turkiyya cikin 'yan makonni masu zuwa.
"Na yi farin cikin ganawa da Philippe Lazzarini, Kwamishina Janar na (UNRWA). Ina fatan aikin da aka gudanar da shi da sadaukarwa ga al'ummar Falasɗinawa zai haifar da sakamako mai kyau da zai kawo ƙarshen wahalhalun da suke ciki," in ji Erdogan a shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal bayan taron da aka yi a fadar shugaban ƙasa.
Lazzarini, shi ma ya nuna godiyarsa, yana mai nuna rawar da matar shugaban ƙasa ke takawa kan batun Falasɗinu.
Jakada Mehmet Gulluoglu, mai kula da ayyukan agajin jinƙai na Turkiyya ga Falasɗinu, shi ma ya halarci taron.
Ofishin Ankara
Ana sa ran UNRWA za ta buɗe ofishi a Ankara cikin 'yan makonni, in ji Lazzarini, yayin da yake magana da manema labarai.
"Mun sanya hannu kan yarjejeniyar ƙarshe da gwamnatin Turkiyya, kuma a wannan karon majalisar ta amince da hakan," in ji shi ga manema labarai, yana mai ƙara wa da cewa "batu ne na ‘yan makonni" za a buɗe.
Wannan matakin ya zo kwana ɗaya bayan da Hukumar Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana fuskantar "mummunar" matsalar kuɗi wanda ya tilasta mata korar ma'aikatanta 571 na Gaza waɗanda suka ci gaba da aiki bayan an kwashe su daga yankin da yaƙi ya daidaita.
UNRWA ta ce shawara "mai matuƙar wahala" wajen yanke wa ta samo asali ne daga matsalolin kuɗi da suka samo asali daga raguwar gudunmawar da ta dogara da ita bayan gangamin da Isra'ila ke yi.
Tsawon shekaru sama da saba'in, hukumar ta samar da taimako da tallafi ga 'yan gudun hijirar Falasɗinawa a faɗin Gaza, Gabar Yamma da aka mamaye, Lebanon, Jordan da Syria, kuma har yanzu tana aiki "duk da ƙuntatawa da yawa," in ji Lazzarini.
A bara, Isra'ila ta haramta wa UNRWA gudanar da ayyuka a cikin ƙasar, kuma Lazzarini ya ce tana kuma neman dakatar da ayyukanta a yankunan Falasɗinawa.
"Akwai sha'awa ga gwamnatin Isra'ila na wargaza UNRWA, don tabbatar da cewa hukumar ba ta da wani matsayi a nan gaba a Gaza da kuma wataƙila a yankunan Falasɗinawa da aka mamaye," in ji shi.