An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Hukumar Kula da Kare Bayanai ta ƙasar ta ci tarar ƙananan hukumomin ne bayan sun karya doka ta hanyar gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan al'ummomin Musulmai ba tare da sun sani ba
Hukumar Kula da Kare Bayanai ta Holland ta AP, ta ci tarar ƙananan hukumomi goma a ƙasar, jumullar euro 250,000 (kimanin $295,000) saboda karya dokokin sirri ta hanyar gudanar da binciken ƙwaƙwaf kan al'ummomin Musulmai ba tare da sun sani ba, in ji gidan rediyon NOS a ranar Alhamis.
A shekarar 2021 ne karon farko da aka fara sanar da cewa ƙananan hukumomin sun ba da umarnin a asirce don gudanar da nazarce-nazarce kuma su yi aiki a kan wasu takardu da suka ƙunshi bayanan sirri game da mazauna Musulmai.
Binciken ya samo asali ne kan fargabar cusa wa jama’a tsattsauran ra’ayi wanda ya samo asali daga Daesh da kuma yaƙin basasar Syria.
Bayan kira daga gwamnati da kuma hukumar yaki da ta'addanci ta ƙasar kan cewa su ɗauki matakan daƙile tsattsauran ra’ayi da kuma daƙile tafiya Syria, ƙananan hukumomi goma sun ɗauki hayar wani kamfani na waje don tattara bayanai kan al'ummomin Musulmai na cikin gida, ciki har da tsarin masallatai da muhimman mutane, in ji AP.
Duk da cewa abubuwan da aka iyakance na rahoton sun sha bambam, duk sun ƙunshi bayanai game da addinin mutane, kamar mazhabar Musulunci da suke bi. Wasu sun kai ga tattara sunaye, hotuna, bayanan iyali da labaran yadda ake gudanar da masallatai, inda a lokuta da dama aka haɗa cikakkun bayanan mutane.
Haka kuma an miƙa wa ‘yan sanda wasu daga cikin rahotannin sannan an miƙa su ga hukumar NCTV da Ma'aikatar Al'amuran Jama'a da Aikin Yi.
“Ƙananan hukumomin ba su da hujjar samun waɗannan bayanai. An keta sirrin mutanen da abin ya shafa matuƙa. Wannan ya lalata amincin ƙananan hukumomi da yawa,' in ji shugaban AP, Aleid Wolfsen.
Kananan hukumomin da za a ci tarar sun haɗa da: Delft, Ede, Eindhoven, Haarlemmermeer, Hilversum, Huizen, Gooise Meren, Tilburg, Veenendaal da Zoetermeer.
Hukumar Kula da Kare Bayanai ta Holland ta ce karya dokokin da suka shafi sirrin jama’a sun kasance masu tsanani saboda sun shafi bayanan addini masu muhimmanci, kuma ta lura cewa kananan hukumomin ba su fahimci nauyin doka da ke kansu yadda ya kamata ba.
Hukumar ta kuma ce ƙananan hukumomin za su amince da tara da aka ci sur, kuma tun a ranar Talata birnin Delft ya nemi gafarar ƙungiyoyin Musulmai na cikin gari, ciki har da Masallacin Al-Ansaar, saboda wannan binciken na sirri.