| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Fidan na Turkiyya ya ce amfani da hare-haren sama ba zai rushe gwamnatin Iran ba
Kalaman na zuwa yayin da Iran da Amurka ke ci gaba da tattaunawa a Oman, inda Ankara take ci gaba da tuntuɓar ɓangarorin biyu domin hana yaƙi na yanki.
Fidan na Turkiyya ya ce amfani da hare-haren sama ba zai rushe gwamnatin Iran ba
Ankara ta yi kira da a bi hanyar diflomasiyya yayin da aka fara tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a Oman / AA
17 awanni baya

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce kai hare-haren sama kan Iran ba zai janyo rushewar gwamnatin ƙasar ba, inda ya yi watsi da iƙirarin da ke cewa matakin soji zai iya kawo sauyin gwamnati.

"A a, ba za ta rushe ba," kamar yadda Fidan ya bayyana a wata hira ta kai-tsaye da kafar CNN Turk ranar Litinin a lokacin da aka tambaye shi kan ko gwamnatin Iran za ta rushe idan aka kai mata harin hamɓarar da ita.

"Ba na so na yi hasashe game da wasu yanayi-yanayi a Iran, amma gwamnatin ba za ta sauya ba ta hanyar harin sama. Wannan mafarkin da ba zai tabbata ba ne," in ji shi .

Fidan ya ƙara da cewa duk da cewa matakin soji zai iya raunata ƙasa, ba zai kawo sauyin gwamnati ba.

"Abin da zai iya faruwa shi ne gwmanatin ta yi rauni, tsarin mulkin ya yi rauni kuma ta gaza iya hidindimu ga mutanenta. A wannan lokacin, gwamnati mai mulki za ta iya ɗaukar matakai masu tsauri domin gyara yanayin, za ta iya sauya kanta," in ji shi.

Tseren diflomasiyya daga Ankara

Kalamansa na zuwa ne yayin da Iran da Amurka ke shirin shiga mataki na gaba na tatatunawa a Oman ranar Jumma’a bayan dakatar da ita na wani lokaci.

Yayin da yake jaddada cewa tashin hankali kan Iran shi ne duniya ta fi mayar da hankali a kai, Fidan ya yi gargaɗin cewa yankin ba zai iya jure wani sabon rikici ba.

"Shugabanmu Recep Tayyip Erdogan ma yana nuna cikakken taka-tsantsan game da wannan lamarin. Saboda haka, muna son mu yi amfani da dukkan hanyoyin da ke akwai domin hana ɓarkewar yaƙi," in ji shi.

Fidan ya ce Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya masa bayani kan tattaunawar kuma ya bayyana cewa Ankara tana tuntunɓar ɓangaren Amurka ma.

Da yake bayyana yanayin a matsayin wani yanayi “da ke da wahalar warwarewa cikin sauri," duk da haka ya bayyana amincewar da ke a fili tsakanin ɓangarorin biyu su ci gaba da tattaunawa.

Ya ce kira da a samar da "mafita ta dabaru" na jan hankali kuma sun jaddada buƙatar da ke akwai ta kaucewa daga "barzanar yaƙi."

"A halin yanzu, babu alamar barazanar yaƙi nan take," kamar yadda Fidan ya bayyana, yana mai cewa an buɗe hanyar tattaunawa.