Sojojin Operation Hadin Kai sun yi wa 'yanta'adda mummunar illa a Jihar Borno, inda suka kashe wani mai ɗaukar bidiyo na ƙungiyar ISWAP.
Haka kuma sun ce sun ƙwato kayayyakin bidiyo da sauran bayanan dijital masu ɗauke da muhimman bayanai kan ayyukan "abokan haɗin gwiwa” da ‘yanta’adda “ƙasashen waje."
A wata sanarwa wadda Mohammed Goni, Mukaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, ya fitar ya ce sojojin sun samu wannan nasara ce bayan da suka daƙile yunƙurin ‘yanta’addan ISWAP na kutsawa yankin Cross Kauwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa a Jihar Borno, inda suka yi musu mummunar illa tare da tilasta musu tserewa cikin ruɗani.
Goni ya ce harin da bai yi nasara ba ya faru ne da misalin karfe 10:20 na dare a ranar 11 ga Yulin 2026, lokacin da 'yanta'addan suka yi yunƙurin amfani da duhun dare domin kutsawa wurin da sojojin suke.
"Sojojin da ke cikin shirin ko-ta-kwana sun gano motsin maharan cikin gaggawa, sannan suka mayar da martani mai ƙarfi, lamarin da ya tilasta wa 'yanta'addan yin watsi da shirinsu na kwasar magungunan cutar kwalara tare da tserewa cikin ɗimuwa bayan sun yi mummunar asara."
Sanarwar ta ƙara da cewa kisan da aka yi wa wani mai ɗaukar bidiyo na 'yanta'addan yayin wannan harin ya bai wa sojojin damar ƙwato na'urar ɗaukar bidiyo ta Sony, wadda ke ɗauke da bayanai masu matuƙar muhimmanci, ciki har da bidiyon ayyukan ta'addanci da kuma kayan yaɗa farfaganda.
A cewar Goni, binciken farko da aka gudanar kan bidiyon ƙarshe da aka ɗauka kafin harin ya nuna cewa manyan kwamandojin ISWAP guda huɗu (Qai'ds) ne suka jagoranci harin tare da masu taimaka wa ta'addanci daga ƙasashen waje guda uku.
Sun haɗa da wani Balarabe ɗan Falasɗinu mai suna Abu Ishaq, wanda ake zargin shi ne babban mai horas da ‘yanta’addan Daesh. Da wani Balarabe ɗan Maroko mai suna Abu Thaiba, wanda likita ne da ke aiki a cibiyar 'yanta'addan.
Sai kuma wani Balarabe wanda har yanzu ba a tantance sunansa ba, in ji Goni.



















