| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta kama “‘yandaba da dilolin ƙwaya” 345 cikin kwana uku
Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar ’YanSanda da ke Bompai ranar Litinin, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne daga ranar 5 zuwa 7 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri.
Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta kama “‘yandaba da dilolin ƙwaya” 345 cikin kwana uku
Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta kama “‘yandaba da dilolin ƙwaya” 345 cikin kwana uku / Kano State Police Command

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutum 345 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka daban-daban a wani samame na musamman da ta gudanar a fadin jihar cikin kwanaki uku.

Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar ’YanSanda da ke Bompai ranar Litinin, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne daga ranar 5 zuwa 7 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri da rahotannin al’umma.

A cewarsa, samamen ya gudana ne a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda jami’an tsaro suka mayar da hankali kan wuraren da ake zargin masu aikata laifuka ke taruwa da kuma wuraren da ake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

CP Bakori ya bayyana cewa baya ga kama mutum 345, rundunar ta kuma ƙwato makamai masu hatsari guda 270, ciki har da wuƙaƙe, adduna, gatari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen aikata laifuka da tayar da zaune tsaye.

Haka kuma, ya ce an samu tarin miyagun kwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol, Pregabalin, da madarar sukudaye wato “Suck and Die” da Turanci, tare da wasu nau’ikan kayan maye daban-daban.

Kwamishinan ya bayyana cewa wannan nasara ta taimaka wajen daƙile ayyukan daba, rage ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma hana wasu manyan laifuka kamar fashi da makami da ƙwacen waya.

Ya danganta nasarar da aka samu da aikin Operation Kukan Kura, wanda ke ƙara yawan sintiri a sassan jihar, da kuma sabon Sashen Yaki da Manyan Laifuka (VCRU), wanda ya ƙara wa rundunar ƙarfin tattara bayanan sirri da kuma saurin kai dauki lokacin gaggawa.

Kwamishina Bakori ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ga masu aikata laifuka ba, yana mai gargadin cewa duk wanda ya ci gaba da shiga harkokin daba ko ta’ammali da miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukuncin doka.

Ya kuma ce yanzu haka ana binciken mutane 345 ɗin da aka kama, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

A karshe, shugaban ’yansandan ya yaba wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano bisa hadin kai da bayar da bayanan sirri, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko abu da suke zargi domin kara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.

Rumbun Labarai
Sake cin zaɓen gwamnan Osun tabbaci ne cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Nijeriya—Tinubu
INEC ta ayyana Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Osun
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da ke ketare su zuba jari a Nijeriya
Tinubu ya yi alƙawarin farfaɗo da matatun man Nijeriya da suka jima ba sa aiki yadda ya kamata
Shugabannin addinai a Nijeriya sun sa hannu kan yarjejeniyar inganta zaman lafiya da fahimtar juna
An gano gawawwaki 9 a Jihar Neja ta Nijeriya, kwanaki bayan ceto mutane 308 da aka yi garkuwa da su
Kaduna, Sokoto, Zamfara da wasu jihohin Nijeriya 10 na fuskantar barazanar ambaliya - NiMet
‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi
'Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 6.6 kan sayen datar waya a cikin shekara ɗaya
Mutane 237 ne suka mutu sakamakon zazzaɓin Lassa a watanni bakwai na 2026 a Nijeriya - NCDC
Sojojin Nijeriya sun kashe Abu Khalid Al Muhajir da wasu  kwamandojin ISWAP tara a Borno
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
Super Falcons da Indomitable Lionesses na gogayyar shiga Gasar Kofin Duniya
Gwamnatin Nijeriya za ta fara sarrafa kayayyakin tsara iyali a cikin ƙasar
Hukumar EFCC ta rufe asusun gwamnatin Jihar Osun kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamna
Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An saki gomman mutanen da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara bayan wata shida a hannun ‘yanta'adda
WAEC ta riƙe sakamakon jarrabawar ɗalibai 167,486
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe