An gabatar da kudiri a Majalisar Dokokin Amurka don saka wa Ƙungiyoyin Miyetti Allah takunkumi
Kudirin ya ambaci kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore a matsayin kungiyoyin da ke da hannu a irin waɗannan laifuka.
An gabatar da sabon kudirin doka a majalisar dokokin Amurka wanda ya tanadi sanya takunkumi da wasu matakai ga mutane da kungiyoyin da ake zargi da aikata manyan laifuka na tauye ‘yancin addini a Nijeriya.
Kudirin ya ambaci Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da Miyetti Allah Kautal Hore a matsayin kungiyoyin da ke da hannu a irin waɗannan laifuka.
Kudirin da Christopher Smith, ɗan majalisar wakilai ya gabatar, ya nemi a sanya takunkumi ga mambobin waɗannan kungiyoyi, ciki har da haramta musu biza da kuma ƙwace kadarorinsu na wucin-gudi.
Ya gabatar da kudirin ne a ranar Talata, inda ya yaba wa shugaban Amurka Donald Trump saboda sake sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ake kira “Country of Particular Concern (CPC)” — ƙasashe da ake kallon suna da matsalolin tsanantar tauye ‘yancin addini.
“Shugaba Donald J. Trump ya yi abin da ya dace kuma cikin gaggawa wajen sake sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen CPC, domin tabbatar da cewa gwamnatin Nijeriya ta ɗauki alhakin rashin tsayawa tsayin daka kan zaluncin addini da masu tsattsauran ra’ayin Musulunci kamar Boko Haram da Fulani masu ta’addanci ke yi.”
A cikin kudirin, Christopher ya bayyana cewa Amurka ta sanya “Ƙabilar Fulani masu dauke da makamai” da ke aiki a jihohin Benue da Filato cikin jerin ‘yan ta’addan da ake saka wa ido) a ƙarƙashin dokar ‘Yancin Addinin Ƙasa da Ƙasa.
Entities of Particular Concern (EPC) na nufin kungiyoyin da ba na gwamnati ba da suka aikata manyan laifuka na tauye ‘yancin addini bisa dokokin Amurka.
Kudirin Christopher ya kuma ba da shawarar cewa Amurka ta bayar da gaggawar tallafin jinƙai kai tsaye ga ƙungiyoyin addini don taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunni a jihohin tsakiyar Nijeriya.