Turkiyya za ta karɓi baƙuncin manyan tarukan duniya a 2026: Shugaban Erdogan
Turkiyya tana shirin shiga shekarar da za ta karbi wasu manyan tarukan duniya a shekarar 2026.
Turkiyya na shirin shiga shekara mai mahimmanci a fagen duniya a 2026, yayin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanar da jerin manyan tarukan kasa da kasa da kasar za ta karɓi baƙuncinsu.
“Turkiyya za ta shaida shekara mai cike da tarukan duniya a 2026, a kowane fanni,” in ji Erdogan a taron Rukunin Majalisar Wakilan Jam'iyyar AK da aka gudanar a ranar Laraba.
Ya ce birnin yawon buɗe ido na Antalya zai karbi kusan kasashe 200 don taron COP31 na sauyin yanayi, yayin da Ankara za ta karɓi bakuncin Taron Shugabannin NATO a watan Yuli.
Turkiyya za ta kuma shirya Taron Kolin na 13 na Kungiyar Kasashen Turkic, in ji Erdogan.
“Akwai yiwuwar samun duniya mafi adalci”
Shugaba Erdogan ya kuma bayyana rawar da kasarsa ke takawa a Taron G20 a Afirka ta Kudu, yana mai nuna nauyin tattalin arzikin wannan rukuni da muhimmancinsa wajen magance manyan kalubalen duniya.
Shugaban Ƙasar ya ce ya yi muhimman ganawa a yayin Taron G20, dandalin da kasashen mambobinsa ke wakiltar kashi 85 cikin 100 na tattalin arzikin duniya da kusan biyu bisa uku na yawan mutanen duniya.
Turkiyya, in ji shi, na ci gaba da neman samar da duniya mai adalci, abin da ya bayyana a goyon bayanta ga kasashe masu karancin kudin shiga lokacin da ta rike shugabancin G20 a 2015 da kuma a sakon da ta gabatar a Johannesburg: “Akwai yiwuwar samun duniya mafi adalci”
Taron NATO
Taron NATO zai gudana a watan Yuli a Ankara, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya za ta shimfida tubalin yanke shawarwari masu "matukar muhimmanci".
A matsayinta na mamba mai muhimmanci a NATO, Turkiyya ta taba daukar bakuncin manyan tarukan kawancen, ciki har da wanda aka gudanar a Istanbul a shekarar 2004.
A taron na baya, shugabanni sun tattauna batutuwa kamar faɗaɗa NATO, ayyukan da ake gudanarwa a Afghanistan da Iraƙi, da kafa Istanbul Cooperation Initiative (ICI) — wani tsarin da aka tsara don tallafa wa tsaro na dogon lokaci a matakin duniya da na yankin ta hanyar ba kasashen da ba mambobin NATO ba a manyan kasashen Gabas ta Tsakiya damar yin hadin gwiwa da Kungiyar.
Taron COP31
Jagorancin Uwargidan Shugaba, Emine Erdogan, a fannin dorewar muhalli ya karfafa ƙoƙarin Turkiyya don yin aiki tare kan sauyin yanayi kuma ya tallafa wa neman daukar bakuncin Taron Bangarorin na 31 (COP31).
Ta zama muryar da ake ji a manufofin muhalli na shirin "Zero Waste" da aka kaddamar a 2017, wanda yake zaburar da sabunta makamashi da rage shara da aiwatar da tsarin tattalin arziki a fadin kasa.
Wannan shiri ya samu Kyautar Ayyukan Manufofin Duniya ta UNDP (Global Goals Action Award) kuma ya kara fitar da martabar Turkiyya a idon duniya.
Erdogan ya kuma shugabanci Kwamitin Shawarwari na MDD na Mataki Mai Girma kan "Zero Waste" kuma ya jaddada cewa daukar mataki kan sauyin yanayi wajibi ne ga rayuwar al'ummomin gaba.
Taron kasashe masu amfani da harshen Turkanci
Taron kolin na 13 na kasashe masu amfani da harshen Turkanci ma za a yi shi a 2026 a Turkiyya, yayin da taron da ya gabata aka gudanar a Azerbaijan.
A yayin taron da ya gabata, Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga kasashen Turkic da su taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiyar da tsaro a yankin.