Likitoci a Nijeriya sun nuna damuwa game da barazanar ƙarancin ma’aikata da fannin kiwon lafiyar ƙasar ke fuskanta, inda likitoci 55,000 ne suka saura domin kula da ‘yan ƙasar miliyan 220.
Sun nuna damuwar ne a taron ƙungiyar likitocin Nijeriyar da suka yi a asibitin ƙwaƙwalwa na tarayya da ke unguwar Yaba a Legas, mai taken, “Likitocin da adadinsu ya yi kaɗan sosai, marasa lafiya da adadinsu ya yi yawa sosai: Sakamakon ƙarancin ma’aikata ga lafiyar ƙwaƙwalwar ‘yan Nijeriya.”
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa likitocin waɗanda akwai ƙwararru a kan lafiyar ƙwaƙalwa a cikinsu, sun kuma ce yanayin da ake ciki a halin yanzu na sa damar samun kulawa daga likitocin ƙwaƙwalwa na ƙara wuya.
Likitocin sun kuma ce aƙalla likitocin Nijeriya 16,000 ne suka fice daga ƙasar cikin shekaru biyar da suka gabata, lamarin da ya daɗa tsananta ƙarancin ma’aikata a fannin lafiyar ƙasar.
Sun yi gargaɗin cewa ci-gaba da ƙaurar ma’aikatan lafiya babu ƙaƙƙautawa ya rage ma’aikatan lafiyar ƙwaƙwalwar ƙasar sosai, lamarin da ya faɗaɗa giɓin da ke akwai da kuma tsadar magani da kuma ƙarin matsi kan ƙwararru kaɗan da ke cikin fannin.
Shugaban ƙungiyar NMA ta likitocin Nijeriya Farfesa Omoti Ernest, ya ce alƙaluma na baya bayan nan sun nuna cewa hukumar kula da likitoci da likitocin haƙori ta Nijeriya MDCN ta yi wa likitoci fiye da 130,000 rijista, amma kimanin likitoci 55,000 kawai ne ke aiki a cikin Nijeriya.
Ya ce ga adadin mutanen da ya zarce miliyan 220, wannan na nufin kimanin likita ɗaya ga kowane mutum 3,600 zuwa 4,000.
“Wannan kason ya yi ƙasa sosai da kason da hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar samarwa na likita ɗaya ga kowane mutum 600, lamarin da ya nuna ƙarancin ma’aikatan kiwon lafiya da kuma matsin da fannin lafiya ke fama da shi
“Da yawa daga cikin likitocin da ke Nijeriya sun fita ko kuma sun daina aikin likitanci, lamarin da ya ƙara ƙarancin ma’aikatan jinya a ƙasar,” kamar yadda shugaban ƙungiyar NMA ɗin ya bayyana.
Ya ce ficewar ƙwararru wajen neman damarmaki masu inganci a ƙetare ya yi tasiri sosai kan asibitocin Nijeriya da kuma ma’aikatan fannin kiwon lafiya.
“Dubban likitoci da sauran ƙwararru a fannin kiwon lafiya sun bar ƙasar cikin ‘yan shekarun nan, lamarin da ya haddasa ƙarancin ma’aikata tare da ƙara yawan ayyuka kan waɗanda suka tsaya inda da yawa ke fama da gajiya da kuma raguwar ingancin kulawar da suke bayarwa a cikin da yawa daga cikin asibitocin gwamnati,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mazauna karkara ne lamarin ya fi shafa tun da suna fama da ƙarancin damar samun kulawa kafin likitocin su fara ficewa.
Ya bayyana cewa dalilan ficewarsu sun haɗa da ƙarancin albashi da rashin ingantaccen yanayin aiki da rashin tsaro da ƙarancin damar ci-gaba a aiki da kuma ƙarancin zuba jari a kayayyakin aikin kiwon lafiya.









