Sudan ta zargi rundunar RSF da aikata 'kisan ƙare-dangi', ta nemi duniya ta ɗauki mataki

Mahukunta a Khartoum sun yi kira ga ƙasashen duniya su sauya daga yin Allah wadai zuwa "ɗaukar ƙwararan matakai da suka dace da doka" domin kare fararen-hula.

By
Sudan ta yi kira ga Duniya ta wuce kamalam nuna damuwa kan lamarin domin ta ƙaƙba tsarin tabbatar da yin daidai / AP

Sudan ta zargi rundunar Rapid Support Forces (RSF) da aikata "kisan ƙare-dangi" kuma ta nemi ƙasashen duniya su ɗauki ƙwararan matakai na hukunci maimakon yin kalaman fatar baki kawai.

"Sudan na gabatar da jawabi ga wannan taro ne a wani lokaci na babban bala’in da ƙasar ke ciki da kuma damuwar ƙasashen duniya mai yawa," in ji ƙaramin jakada Faisal Abdelazim Salim Mohamed a wani babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi domin shekara ta goma ta tunawa da martaba waɗanda aka yi wa laifin kisan ƙare-dangi.

Ya ce fararen-hula a Al Fasher da ma wasu wurare an yi musu kisan gilla da cin zarafinsu da raba mutane da gidajensu da lalata hujjoji na aikata laifuka.

"Laifukan da aka aikata, idan aka duba yawansu da niyyarsu, sun cika ma’anar kisan ƙare-dangi a shari’ance," in ji shi.

"Waɗannan laifuka da dakarun RSF suka yi ba a ɓoye suke ba. Suna nan a rubuce. A bayyane suke. Kuma sun buƙaci fiye da bayyana damuwa kawai. Suna neman a bi musu haƙƙoƙinsu."