| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojin Nijeriya sun halaka ‘yanta’adda 50, sun yi asarar dakaru biyu yayin daƙile harin ISWAP a Yobe
Harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2026, lokacin da ‘yanta’addan suka kai farmaki daga sassa daban-daban a cikin duhun dare.
Sojin Nijeriya sun halaka ‘yanta’adda 50, sun yi asarar dakaru biyu yayin daƙile harin ISWAP a Yobe
Wasu daga cikin makaman da sojojin Nijeriya suka ƙwato / Nigerian army

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas Operation HADIN KAI sun dakile wani harin haɗin gwiwa da mayaƙan ISWAP suka kai hedikwatar Brigade ta 27 da kuma shingen bincike na Buni Gari a Jihar Yobe, inda aka kashe aƙalla ‘yanta’adda 50 a yayin artabun.

Harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 8 ga watan Mayun 2026, lokacin da ‘yanta’addan suka kai farmaki daga sassa daban-daban a cikin duhun dare.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce ‘yanta’addan sun fara kai hari daga ɓangaren yamma kafin su ƙara tura mayaƙa daga kudanci ta hanyar Ganinga Junction sannan daga kudu maso yamma domin kewaye dakarun.

Sai dai ya ce dakarun sun tsaya tsayin daka tare da mayar da martani da manyan makamai da dabarun yaƙi da suka tilasta wa maharan ja da baya cikin ruɗani.

Operation HADIN KAI ta kuma tabbatar da rasuwar sojoji biyu a yayin artabun, inda ta bayyana su a matsayin jarumai da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare ƙasa.

Sojojin sun ce an gano gawarwakin ‘yanta’adda guda 10 a kusa da sansanin, yayin da rahotannin sirri suka nuna cewa an gano fiye da gawarwaki 20 a hanyoyin da suka bi wajen tserewa ta yankunan Gashua, Azare da Kamuya.

Rundunar sojin sama ta OPHK ma ta kai hare-haren sama kan ‘yanta’addan da ke guduwa, inda ta kashe kusan mayaƙa 20.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda takwas, bindigogin GPMG guda biyu, roka guda biyu, bama-baman RPG, jigidar harsasai, da kuma kwalaben na’urorin tayar da bama-bamai na IED guda uku.

Sojojin sun kuma bayyana cewa wasu motocin kariya daga hare-haren bama-bamai na MRAP da motocin yaƙi sun lalace yayin musayar wuta, yayin da jami’an da suka jikkata ke samun kulawar lafiya kuma suna cikin yanayi mai kyau.

Rundunar ta ƙara da cewa dakaru tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai na ci gaba da gudanar da sintiri da bincike a yankin domin farautar ‘yan ta’addan da suka tsere tare da hana su sake haɗuwa.

Rumbun Labarai
Dakarun tsaro sun ƙwace makamai a jihar Kogi ta Nijeriya tare da kama mutum uku
Dakaru sun kassara 'yanta'adda da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a samame a Sokoto da Katsina
Yadda bankunan Nijeriya da kwastomominsu suka yi asarar naira biliyan 134 a zambar intanet
'Yanta'adda sun kashe manoma 11 a arewa maso gabashin Nijeriya
Ana gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Ekiti da ke kudancin Nijeriya
Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a karo na biyu
Rashin hukunta masu laifi na ƙara haifar da zarge-zargen kisan kare-dangi a Nijeriya: MDD
Tsoffin janar-janar a Nijeriya sun nemi a yi wa harkar tsaro garambawul bayan rasuwar Rabe Abubakar
ACF: Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa ta yi Allah wadai da 'cin zarafin mata' 'yan arewacin Nijeriya a Ondo
Kotun Birtaniya ta wanke tsohuwar ministar mai ta Nijeriya Diezani daga tuhumar cin hanci da rashawa
Japa: Likitoci 55,000 kawai suka saura wa 'yan Nijeriya miliyan 220 — Ƙungiyar Likitoci
Sojojin Nijeriya sun ceto mutum hudu da aka sace daga gungun 'yanta'adda a Katsina
Shugaba Tinubu ya amince a ɗauki jami'an kare daji 1,000 a Jihar Katsina
Kotu ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin soke rijistar jam'iyyar ADC da wasu jam'iyyu
Nijeriya ta kama mutane takwas saboda yaɗa labarai marasa tushe
Bankin Duniya ya ayyana tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tincan cikin 20 da suka fi inganci a duniya
'Yanbindiga sun kashe aƙalla mutum 20 Jihar Kebbi ta Nijeriya
ADC ta yi watsi da cire ta daga rijista, ta sha alwashin kalubalantar hukuncin kotu
Kotun Nijeriya ta ba INEC umarnin soke rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu
Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da fiye da mutum 400 a kotu a Abuja kan zarginsu da ta'addanci