| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Cibiyar Ayyukan Sojan Amurka ta aiwatar da jerin hare-hare a Iran bayan harbo jirgin yaƙin Amurka mai saukar angulu a cikin dare.
Amurka ta kai hare-hare da dama ta sama Iran yayin da hankula suka tashi kan sake ɓarkewar yaƙi
Wani jirgin yakin rundunar sojan saman Amurka samfurin F-15E Strike Eagle yana tashi daga wani sansani a Gabas ta Tsakiya. (Hoto: FILE) / Reuters

Amurka ta ƙaddamar da gagarumin hararin bama-bamai ta sama a kan Iran, kwana guda bayan da aka harbo wani jirgi mai saukar ungulu na yaƙi na Amurka kusa da Mashigar Hormuz.

Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya bayyana cewa an ji sautin bama-bamai da jiniyar tsarin tsaron sararin samaniya a garuruwa da dama da ke gaɓar tekun Iran, ciki har da birnin Sirik da kuma tsibirin Qeshm.

Cibiyar ayyukan sojin ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata cewa, "hare-haren kare kai" sun fara ne da misalin karfe 5 na yamma agogon Washington, bisa umarnin Trump.

"Wannan aiki ne na mayar da martani da ya dace kan tsokanar da Iran ta yi ba tare da wani dalili ba," in ji rundunar a cikin wata sanarwa.

Kamfanin dillancin labarai na Mehr na Iran, wanda ya ambato mazauna yankin, ya bayar da rahoton fashewar manyan bama-bamai a yankin Sirik.

Kafofin watsa labarai na gwamnatin Iran sun ruwaito cewa an kuma kai hari a tsibirin Qeshm da kuma tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas.

Trump ya sha alwashin mayar da martani

“Ina jin yana da matuƙar muhimmanci a mayar da martani. Sun harbo helikwafta, mu kuma muna mayar da martani a daidai lokacin da muke magana,” Trump ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta ABC News game da hare-haren na ramuwar gayya da Amurka ke kai wa Iran.

"Wannan martani ne ga abin da suka yi... ga helikwafanmu a daren jiya, kuma na yi amanna cewa martanin ya kamata ya kasance mai ƙarfi sosai, mai cike da nuna iko, kuma abin da wannan harin yake yi kenan," in ji shugaban na Amurka.

A gefe guda kuma, shafin yanar gizo na kafar labaran Axios, ya ambato wani babban jami'in Amurka, yana cewa dakarun sojin Amurka sun kai hari kan wasu batirorin kariyar sararin samaniya da na'urorin kula da jirage na Iran a kewayen Mashigar Tekun Hormuz.

Axios ya ce zagaye na biyu na hare-haren a Iran yana gudana "yanzu haka" wanda ke nufar tsarin tsaron sararin samaniya da na'urorin kula da jirage.

Rumbun Labarai
Iran ta kai manyan hare-haren makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a Gabas ta Tsakiya
Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran ta sanar da rufe Mashigar Ruwan Hormuz 'sai abin da hali ya yi'
Jagoran Addinin Iran ya sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan da aka yi wa Ali Khamenei
Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za 'hallaka da lalata' Iran idan Tehran ta kai masa hari
Masu shiga tsakani suna fafutukar kwantar da tankiya tsakanin Amurka da Iran
Turkiyya da Iran sun tattauna kan halin da yankin ke ciki, da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran
Akwatin gawar Khamenei ya isa Mashhad a yayin da Iran ke shirin taron jana’iza na ƙarshe
Iran ta harba makamai masu linzami kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz: Rahoto
Miliyoyin mutane sun halarci jana’izar Khamenei a Tehran
Pezeshkian ya soki shirun duniya bisa matakan Isra'ila yayin da aka fara taron jana'izar Khamenei
An kai gawar Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei Tehran don yin taron bankwana
Aƙalla yara 21,000 aka kashe a Gaza cikin kwana 1,000 na yaƙin Isra’ila: Ƙungiyar Save The Children
Qatar ta kashe dala mafi yawa, in ji Trump lokacin da ya hau jirgin da Doha ta ba shi kyauta
Trump ya ce an shirya tattauna ta kai-tsaye tsakanin tawagogin Amurka da Iran, amma Iran ta musanta
Yarjejeniya a cikin sabani: Ɓangarorin da Amurka da Iran suka gaza cim ma matsaya
'Ko ba daɗe ko ba jima': Ministan Isra'ila ya yi barazanar yaƙi ga Syria, suna haƙon Turkiyya
‘Isra’ila ta yi niyyar kashe kowa’: Harin da Amurka ta boye, kuma ba a taba bayyana shi ba
Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna sun cinna wa masallatai biyu wuta a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Amurka da Iran sun amince su kawo ƙarshen yaƙi. Amma akwai wanda za a iya cewa ya yi nasara?
Trump ya sanar da cim ma yarjejeniyar Iran mai tarihi, ya yi alƙawarin buɗe Mashigar Hormuz nan-take