| Hausa
SIYASA
4 minti karatu
Hukunce-hukuncen Kotu da makomar jam'iyyun adawa a Nijeriya
Ficewar wasu daga manyan ’yan hamaya daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC ne ya kara fito da mawuyacin halin da ’yan’adawa ke ciki a a fafutikarsu ta neman korar gwamnati mai ci.
Hukunce-hukuncen Kotu da makomar jam'iyyun adawa a Nijeriya
Hukunce-hukuncen Kotu da makomar jam'iyyun adawa a Nijeriya / Others

Aski ya zo gaban goshi a fagen siyasar Nijeriya, a daidai lokacin da lamura ke kara dagulewa ‘yan hamayya masu neman kwace Mulki daga gwamnatin kasar a zaben shekara mai zuwa. Da damansu sun bazama neman mafita, wanda wasu suke ganin tamkar bulayi kawai suke yi.

Ficewar wasu daga manyan ’yan hamaya daga jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC ne ya kara fito da mawuyacin halin da ’yan’adawa ke ciki a a fafutikarsu ta neman korar gwamnati mai ci.

Hukuncin da kotun ƙolin Nijeriya ta yanke a makon da ya gabata ne ya dagula wa ’yan’adawar lissafi musamman ganin cewa wadanda suka sauya shekar suna kafa hujja da batun shari’un da ake yi a matsayin dalilinsu na fita da jam’iyyar ADC din.

Ko da yake jam’iyar ADC na ganin ta samu abin da ta ke so a yanzu, wato Hukumar Zaben Kasar (INEC) ta mayar da sunan shugabanninta ɓangaren David Mark, amma kuma ana ganin da sauran rina-a-kaba, saboda wani ɓangare na hukuncin kotun ƙolin da ya buƙaci su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari’ar da suke yi da bangaren Nafiu Bala Gombe, abin da masana ke cewa a nan ne gizo yake sakar.

A bayanansu na ficewa daga ADC, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun ambaci rashin tabbas da rikicin shugabanci a matsaayin dalilansu na ficewa daga ADC.

Kazalika ita ma jam’iyar PDP tana fama da irin wannan matsala ta shari’a da rarrabuwar kawuna, inda kotun ƙolin kasar ta rushe shugabancinta ɓangaren Tanimu Turaki da taron da suka gabatar na zaɓen shugabanni a birnin Ibadan a ƙarshen shekarar 2025.

A hannu guda kuma shi ma gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya ɗauko Jam’iyyar APM bayan da ya bar PDP saboda turka-turkar da take ciki.

Masani kan harkokin siyasa kuma malami a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) Dokta Sani Sani Ibrahim ya bayyana abuuwan da suke faruwa da jam’iyyun hamayya da wani yunkuri na ruguza adawa a kasar.

 A watannin da suka wuce ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da ma sauran waɗanda ake ganin za su iya yin tasiri a ɓangare adawa suka dunƙule a jam’iyya ɗaya wato ADC.

Sannan a wani taro da suka yi kwanan nan a birnin Ibadan, kusan gaba daya jam’iyyun hamayyar kasar sun amince cewa dan Takara daya za su tsayar wanda zai kalubalanci shugaba Bola Tinubu.

To sai dai duba da yanayin da ake ciki yanzu da yadda lamura ke kara dagulewa zai yi wuya manyan jam’iyyun hamayyar su tsaya kan maganar tasu.

Kafin yanzu masana harkokin siyasa da dama na ganin dunƙulewar ’ƴan’adawar za ta zamar wa jam’iyyar APC babban kalubale a zaben 2027, watakila ma ya yi silar kawo karshen mulkin jam’iyyar na kusan shekaru 12 a kasar.

Sai dai a yanzu a mahangar masana kimiyyar siyasa, ficewar Kwankwaso da Obi daga ADC zai rage tasirin ’yan’adawa sosai, saboda yadda kawuna da kuri’u za su kasance a rarrabe a lokacin zabe, abin da kuma zai yi wa jam’iyyar APC dadi, saboda hakan zai share mata hanyar sake yin nasara a zabe mai zuwa.

Ko da yake da ma can akwai masanan da suke ganin cewa ko da babu wannan kalubale na hukunce-hukunce kotuna, zai yi wuya manyan jagororin ’yan hamayya su ci gaba da dunkulewa waje guda saboda kowane daga cikinsu yana neman takarar shugabancin kasa ne.

Kuma zai iya fita daga hadakar matukar bai samu biyan bukatarsa ba a zabe mai zuwa.

Dokta Sani ya ce idan har suna so su kai gaci, to dole ne ‘yan hamayyar su fifita muradun al’ummar kasar, maimakon bukatun kanshin kansu da dagawa a kan sai na yi, sannan su dunkule waje guda yadda za su yi karfi sosai, har su iya cim ma burinsu.

Idan kuwa ba haka tamkar ta fadi ne gasassa ga jam’iyya mai mulki.