Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ƙasashe kan fuskanci jarabawa kafin su kai ga samun ci gaba mai girma, yana mai cewa Nijeriya na cikin irin wannan lokaci a tarihinta yanzu.
'Yan'uwana 'yan Nijeriya, al'ummomi da yawa sun shiga jarabawa a tarihi kafin su daukaka. Nijeriya na fuskantar irin wannan jarabawa a yau. Amma ina da yakinin za mu fito daga wannan hali da karfinmu da hadin kai da wadata fiye da a baya.
“Mu ci gaba da wannan tafiya tare. Mu gina Nijeriya mai tsaro, mai wadata, mai haɗa kowa da kowa, kuma wadda ake girmamawa a duniya. Mu ci gaba da gaskata alkawarin ƙasarmu,” in ji Tinubu.
Ya jaddada cewa wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon manyan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar za su haifar da sakamako mai kyau a ƙarshe.
“Ina sane sosai da irin sadaukarwar da ake yi, kuma ina tabbatar muku cewa: sadaukarwarku ba ta tafi a banza ba. Yau kuma zan iya faɗa da kwarin gwiwa cewa Nijeriya ta samu daidaito kuma tana ci gaba gaba,” in ji shugaban ƙasar.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji manyan matsalolin tattalin arziki da tsarin mulki, ciki har da matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati, tallafin man fetur, raguwar kuɗaɗen shiga, matsalolin canjin kuɗi, ƙaruwar biyan basussuka, rashin tsaro da kuma raguwar amincewar jama’a ga hukumomi.
A cewarsa, Nijeriya na kashe har Naira biliyan 18.4 a rana wajen tallafin man fetur a lokacin da tsarin ya kai ƙololuwa, wanda ya zarce Naira tiriliyan 4 a shekarar 2022 kaɗai.
Ya ce kuma tsarin canjin kuɗi daban-daban da damfara a harkar forex sun jawo asarar sama da Naira tiriliyan 8 cikin shekaru uku.
“Lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, ƙasarmu na fuskantar manyan matsalolin tattalin arziki da tsarin gudanarwa.
“Matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati, tallafin man fetur da ba zai dore ba, raguwar kuɗaɗen shiga, matsalolin canjin kuɗi, hauhawar kuɗin biyan basussuka, rashin tsaro a wasu sassan ƙasa, matsalolin samar da makamashi da kuma raguwar amincewar jama’a ga hukumomi duk sun yi barazana ga ci gabanmu.
“A lokacin da tsarin tallafin man fetur ya kai ƙololuwa, Nijeriya na kashe har Naira biliyan 18.4 a rana wajen tallafin fetur — sama da Naira tiriliyan 4 a shekarar 2022 kaɗai — kuɗaɗen da za a iya amfani da su wajen gine-ginen hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, gidaje da sauran muhimman ababen more rayuwa.
“Tsarin canjin kuɗi daban-daban da damfara a harkar forex sun haifar da manyan matsaloli, inda Najeriya ta yi asarar sama da Naira tiriliyan 8 cikin shekaru uku sakamakon anfani da tsarin da kuma hasashe marasa amfani.”
Shugaban ya kare matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, yana mai cewa sun zama dole domin hana durƙushewar tattalin arziki.
“Halin da ake ciki ya buƙaci mataki cikin gaggawa da ƙarfin hali. Dole ne a ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin daidaita tattalin arziki da hana ƙasar fadawa cikin babban rikici.
“Zaɓin hanya mai sauƙi zai iya zama mai daɗin siyasa. Amma shugabanci na buƙatar ƙarfin hali, musamman idan yanke shawara madaidaiciya yana da wahala.
“Da a ce mun ƙi ɗaukar mataki, da ƙasarmu ta fada cikin rugujewar tattalin arziki, ƙaruwar talauci da matsananciyar rashin tabbas. Tare muka zaɓi gyara maimakon rushewa, da kuma ɗaukar mataki maimakon jinkiri. Mun zaɓi farfaɗowar ƙasa na dogon lokaci maimakon jin daɗin ɗan lokaci,” in ji shi.
Yayin da ya amince da tasirin sauye-sauyen kan talakawa, Tinubu ya ce tsadar rayuwa ta jefa iyalai, ma’aikata da ‘yan kasuwa cikin matsin lamba, yayin da matasa da dama suka rasa kwarin gwiwa wajen neman aiki.
“Waɗannan matakai sun zo da sadaukarwa. Tsadar rayuwa da ta biyo bayan manufofinmu ta jefa iyalai, ma’aikata da ‘yan kasuwa cikin matsin lamba.
“Matasa masu neman aiki sun shiga damuwa. Da yawa sun fara tambayar ko waɗannan matakai masu wahala za su kai ga kyakkyawar makoma.”
Shugaban ya bayyana abin da ya kira ci gaba a tattalin arziki, yana cewa kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta samu babban bunƙasa tun daga shekarar 2023.
“Tattalin arzikinmu yanzu ya fi ƙarfin gasa kuma ya fi samun damar ci gaba mai ɗorewa fiye da yadda yake a 2023.
“Kuɗaɗen gwamnati na inganta. Jihohi da ƙananan hukumomi na samun ƙarin kuɗin zuba jari ga jama’arsu. Amincewar masu zuba jari na ƙaruwa.
“Kasuwar hannayen jari na bunƙasa, inda All Share Index ya tashi daga 53,000 da jarin kasuwa na Naira tiriliyan 30 a 2023 zuwa rikodin All Share Index na 250,000 da jarin kasuwa na Naira tiriliyan 160 a wannan shekarar. Kamfanoni na bayyana ribar tarihi da kuma rabon kuɗi.”
Tinubu ya kuma yi magana kan ayyukan gine-ginen ababen more rayuwa a faɗin ƙasar, yana cewa sama da kilomita 2,700 na manyan hanyoyi suna ƙarƙashin ginawa, sake ginawa ko gyarawa.
Ya ambaci wasu daga cikin ayyukan da suka haɗa da hanyar Lagos-Calabar Coastal Highway, Sokoto-Badagry Super Highway, hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, hanyar East-West da kuma hanyoyin karkara da dama.
“Muhimman ayyukan ababen more rayuwa na ci gaba a matakin da ba a taɓa gani ba. Sama da kilomita 2,700 na manyan hanyoyi suna ƙarƙashin ginawa, sake ginawa ko gyarawa.
“An riga an kammala wasu muhimman sassa ko kuma suna gab da kammaluwa, wanda hakan ke sauƙaƙa sufuri, rage lokacin tafiya, bunƙasa kasuwancin yankuna da kuma samar da dubban ayyukan yi.
“Ayyukan sabunta layin dogo na ci gaba domin inganta haɗin kai, harkokin sufuri da haɗa tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.”
Game da harkar mai da gas, Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun jawo sababbin jarin biliyoyin daloli tare da dawo da amincewar manyan kamfanonin mai na duniya.
“Sauye-sauyen da muka aiwatar sun jawo biliyoyin daloli na sababbin jarin manyan kamfanonin mai na duniya waɗanda suka guji ƙasarmu a baya.
“Aikin NLNG Train 7 na dala biliyan 5 na gab da kammaluwa domin ƙara ƙarfin samar da LNG, fitarwa da kuma ribar ƙasa.
“Ana faɗaɗa amfani da gas a cikin gida. Ƙarfin tace mai a cikin gida ya inganta tsaron makamashinmu,” in ji shugaban ƙasar.
















