Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyar Benin

Shugaba Patrice Talon, wanda ake sa ran zai sauka daga mulki bayan shafe wa’adi biyu na shekaru biyar-biyar, ya amince da ministan kudi na ƙasarsa a matsayin wanda yake so ya gaje shi a wannan zaɓe.

By
Shugaba Talon zai sauka ne daga mulki bayan wa’adi biyu na shekaru biyar-biyar, kuma ya amince da Ministan Kuɗi, Romuald Wadagni, domin ya gaje shi. / Reuters

A ranar Lahadi ne mutanen Jamhuriyar Benin suke kaɗa ƙuri’a don zaɓar sabon shugaban ƙasa, inda kusan masu kaɗa ƙuri’a miliyan takwas ke da damar zaɓar mutim da zai maye gurbin Shugaba Patrice Talon.

Shugaba Talon zai sauka ne daga mulki bayan wa’adi biyu na shekaru biyar-biyar, kuma ya amince da Ministan Kuɗi, Romuald Wadagni, a matsayin wanda yake so ya gaje shi.

Yawan fitowar masu zaɓe zai kasance babban al’amari mai muhimmanci, bayan yakin neman zaɓen da bai yi armashi ba sakamakon rashin sha’awar masu zaɓe.

Wadagni, wanda manyan jam’iyyu biyu masu mulki ke marawa baya, ana sa ran zai yi nasara cikin sauƙi. Yana takara ne da Paul Hounkpe, wani ɗan adawa wanda kamfen ɗinsa bai ɗauki hankali ba sosai, kuma wanda ya buƙaci taimakon ’yan majalisa daga ɓangaren masu rinjaye domin samun amincewar da ake buƙata don tsayawa takara.

Babbar jam’iyyar adawa ta “The Democrats” ba ta tsayar da ɗan takara ba, domin shugabanta, Renaud Agbodjo, ya kasa samun adadin amincewar ’yan majalisar da ake buƙata don shiga takarar.

Gibin tsakanin mawadata da talakawa, sai batun bunƙasar tattalin arziki

Masu rinjaye na ɓangaren gwamnati sun ɗora alhakin rashin shigar jam’iyyar “The Democrats” cikin zaɓen ga rarrabuwar kawuna na cikin gida. Wasu manyan jami’ai a jam’iyyar sun koma gefen Wadagni don taya shi kamfen.

Zaɓen Jamhuriyar Benin na gaba zai gudana ne kawai a shekarar 2033, sakamakon garambawul ga kundin tsarin mulki da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda ya tsawaita wa’adin shugaban ƙasa daga shekaru biyar zuwa bakwai, sannan aka haɗa lokacin dukkan zaɓuka su gudana a lokaci guda a wannan shekarar.

Shi kuwa Hounkpe, ya yi alƙawarin sakin “fursunonin siyasa.”

Ƙasar ta ga gagarumar bunƙasa a cikin shekaru goman da Talon ya yi yana mulki: Arzikin ƙasar (GDP) ya ninka sau biyu, bunƙasar tattalin arziki ta wuce kashi 6% kowace shekara, fannin yawon buɗe ido ya faɗaɗa, sannan an kammala ayyukan more rayuwa da dama.

Wadagni, wanda shi ne ya tsara wannan ci gaba a cikin shekaru goman da ya yi a ma’aikatar kuɗi, shi ne ke wakiltar ci gaba da manufofin shugaba mai ci.

Duk da haka, har yanzu akwai manyan ƙalubale, ciki har da gagarumin gibin da ke tsakanin mawadata da talakawa.

Ƙalubalen tsaro

Wani na kusa da Wadagni ya ce, “Mataki na gaba na ci gaban ƙasar shi ne kawar da bakin talauci. Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba.”

An kiyasta talauci ya haura kashi 30 cikin 100, kuma ’yan Benin da dama na korafin cewa amfanun bunƙasar tattalin arzikin da aka samu a cikin shekaru goman da suka gabata bai kai gare su ba.

Haka kuma, bunƙasar tattalin arzikin Benin zai dogara ne kan samar da tsaro da daidaiton ƙasar.

Arewacin Benin na fama da tasirin hare-haren ’yan ta’adda da ke kashe-kashe, waɗanda ke yaɗuwa daga ƙasashe masu makwabtaka da kasar wato Burkina Faso da Nijar.

Idan aka zaɓi Wadagni a ranar Lahadi, ana sa ran zai samu cikakken goyon bayan rundunar soji, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunƙurin juyin mulkin da aka so yi wa Talon a watan Disamban bara.