Ƙasar Amurka tana duba yiwuwar kai wa Iran sabbin hare-hare bayan rushewar tattaunawar zaman lafiya da suka yi a Pakistan, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito.
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance da tawagarsa sun jagoranci tattaunawar a Islamabad, amma ba su cim ma matsaya ba.
Shugaba Donald Trump da masu ba shi shawarwari sun yi nazari kan ƙaddamar da sabbin hare-haren soji a Iran tare da rufe Mashigar Hormuz a matsayin wata hanya ta karya lagon Iran, kamar yadda jaridar ta ruwaito ranar Lahadi.
Da yake magana a wurin shaƙatarwarsa a Florida, Trump ya shaida wa Fox News cewa za a iya kai hare-hare kan tashoshin makamashin Iran da na samar da ruwan sha idan ƙasar ta ci gaba da tsayawa kan bakanta.

Da yake magana a wurin shaƙatarwarsa a Florida, Trump ya shaida wa Fox News cewa za a iya kai hare-hare kan tashoshin makamashin Iran da na samar da ruwan sha idan ƙasar ta ci gaba da tsayawa kan bakanta.
Dabarar rufe Mashigar Hormuz
Mai magana da yawun Fadar White House Olivia Wales ta ce shugaban "ya yi dabara ta gabatar da dukkan zaɓin da ke hannunsa a kan teburin tattaunawa," yayin da take tabbatar da cewa Amurka za ta rufe Mashigar ruwan Hormuz ne domin kawo ƙarshen "ƙwacen kuɗin da Iran take yi wa masu jiragen ruwa."
Washington na neman Iran ta kawo ƙarshen dukkan nau’i na sarrafa yuraniyom kuma ta yi fatali da duk kayayyakin aikinta na ƙeta nukiliya.
Sai dai Iran ta ce ba za ta daina shirinta da bai saɓa wa doka ba.












