Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a ranar Talata a gaban wata Kotun Gundumar Tel Aviv a karo na 81 tun bayan soma shari'arsa a shekarar 2020 don amsa tuhumar cin hanci da rashawa da ake yi masa.
Zuwa kotun na zama karo na farko da Netanyahu ya bayyana a kusan watanni biyu tun bayan barkewar yaki da Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
An dai shirya bayyanar Netanyahu a gaban kotun a ranar Litinin, amma sai ya nemi a soke zaman, saboda "dalilai na tsaro," in ji shi, kafin ya yi zaman shawarwari kan tsaro da suka shafi yakin Lebanon.
Jaridar Isra’ila Maariv ta ruwaito cewa Netanyahu yana matakin ƙarshe na shaidarsa, bayan ba da shaida sama da kwanaki 80 na zaman sauraren kara.
Jaridar Isra'ila ta Maariv ta ruwaito cewa Netanyahu yana gab da kammala matakin shari'arsa na ƙarshe, bayan ya gabatar da shaidu a fiye kwanaki 80 na zaman sauraren ƙara.
A cewar ofishin mai gabatar da kara, har yanzu yana da sauran kimanin kwanaki 11 na bayar da shaida, ban da wani takaitaccen bincike da lauyoyin da ke kare shi za su yi.
"A cikin makonni biyu da suka gabata, an soke zaman sauraron ƙararsa bisa bukatarsa, kuma tunbayan soma yaki da Iran, bai ba da ba’asi a tuhumar da ake yi masa ba, duk da cewa an maido da dukkan zaman sauraron kararraki a kotunan Isra'ila," in ji jaridar.
An shirya Netanyahu zai bayar da shaida a ƙarar shari'ar 4000, inda ake zarginsa da cin hanci, zamba, da kuma keta cin amana, a cewar jaridar.
A tuhumar da ake yi masa, ana zargin Netanyahu da alakar cin hanci da rashawa da ɗan kasuwa Shaul Elovitch, tsohon mallakin kafar jaridar Walla.
Kazalika a tuhumar, ana zargin Netanyahu da iyalansa da gabatar da buƙatu daban-daban a tsarin yada labarai wadanda suka yi daidai da ra’ayinsu da kuma neman a danne abokan hamayyar siyasa.
Zaman kotun ya zo ne a daidai lokacin da aka samu rarrabuwar kawuna a Isra'ila kan rahotannin da ke cewa Netanyahu ya nemi afuwa daga shugaban Isra'ila Isaac Herzog.
A ranar 30 ga Nuwamba, Netanyahu ya nemi afuwa ba tare da ya amsa laifinsa ko kuma ya sauka daga harkokin siyasa ba.
Cin hanci, zamba da kuma cin amana
Tun lokacin da aka soma shari'arsa a shekarar 2020, Netanyahu ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa, yana mai bayyana su a matsayin wani "gangamin siyasa" da ya guduri aniyar cire shi daga mukaminsa.
Dokar Isra'ila ba ta ba da damar yin afuwa ga shugaban ƙasa ba, ba tare da ya amince da laifinsa ba.
Netanyahu na fuskantar tuhume-tuhume uku na cin hanci da rashawa da kuma cin amana wadanda aka yi musu lakabi da Shari'o'i 1000, 2000, da 4000, kuma an shigar da karar ne a watan Nuwamban 2019.
Shari'a ta 1000 ta kunshi zarge-zargen cewa Netanyahu da iyalansa sun sami kyaututtuka masu tsada daga attajirai 'yan kasuwa don samun alfarma.
Sai shari'a ta 2000, inda ake zarginsa da cim ma yarjejeniya da Arnon Mozes, mawallafin jaridar Yedioth Ahronoth, don wallafa labarai masu kyau wadanda suka yi daidai ra’ayinsa.
Tuhume-tuhumen da ake yi masa a wadannan shari'o'in sun soma ne tun daga shekarar 2020 kuma ana ci gaba da gudanar da su.
Baya ga tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa, tun a shekarar 2024 ake neman Netanyahu a Kotun hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) saboda zargin laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza, inda aka kashe mutane fiye da 72,000 a munanan hare-hare da Isra'ila ta yi ta kai wa tun daga watan Oktoba na 2023.
















