TRT ta fice daga taron EBU a yayin da mahalarta suka yi ce-ce-ku-ce kan shigar Isra'ila Eurovision
Kafar watsa labaran ta soki Isra'ila game da ci gaba da take yi da halartar taron a yayin da take yin yaƙin kisan ƙare-dangi a Gaza, inda mambobi da dama daga Turai suka ƙaurace wa taron Eurovision 2026.
Ce-ce-ku-ce ya ɓarke a wurin babban taron ƙungiyar watsa labaran Turai (EBU) na 95 a birnin Geneva kan kasancewar Isra’ila cikin gasar waƙar Eurovision , inda mambobi suka tattauna sabbin dokokin shiga gasar da kuma matsayar kafar watsa labarai mallakar Isra’ila KAN a 2026.
Kafin a fara ƙada ƙuri’u, mambobi sun gabatar da bayanai kan ko kafar KAN za ta iya ci gaba da kasancewa cikin gasar yayin da Isra’ila ta ci gaba da ƙaddamar da kisa ƙare-dangi a Gaza.
Da take magana a matsayar daga cikin mambobin da suka kafa ƙungiyar EBU, kafar TRT mai TRT World ta ce halin da ake ciki a Gaza ya sa halartar Isra’ila ta ci karo da ɗabi’un Eurovision.
"Kamar kowa a cikin wannan ɗakin taron, mu a TRT mun ga gomman shekarun zalunci da kuma kisan ƙare-dangin da ke faruwa a idon duniya," in ji wakilin.
"Tun lokacin da abar da ake kira yarjejeniyar tsagaitar ta fara aiki, an kashe gomman yara kuma har yanzu agaji ba ya iya isa Gaza cikin aminci ba. Isra’ila ta kashe ‘yanjarida fiye da 270. Matsayarmu a bayyane take: bai wa KAN damar shiga [gasar Eurovision] bai dace da ɗabi’un gasar ba."
Ƙarin ƙasashe sun ƙaurace
Kafar RTÉ ta ƙasar Ireland ta maimaita irin wannan matsayar, tana mai cewa: "Idan aka yi la’akari da rasa rayukan mai muni da aka yi a Gaza da kuma matsalar jinƙai da ke faruwa, mun yi imanin cewa ba zai dace mu kasance a cikin gasar ba idan KAN ta Isra’ila za ta shiga."
A lokacin da kafar watsa labaran Isra’ila ta hau dandali, wakilan TRT fice daga cikin ɗakin taron a domin nuna rashin jin ɗaɗinsu.
TRT da wasu mambobin sun yi adawa tsarin ƙada ƙuri’a a bayyane kua sun nemi a ƙada ƙuri’a a asirce.
Daga baya, taron ta amince da sabbin dokokin shiga gasar sai dai kuma ta yanke shawarar cewa ba za ta ƙada ƙuri’a ba kan ko Isra’ila za ta shiga ko a’a.
Mambobin na Jamus da Austria sun bayyana goyon bayansu ga KAN, yayin da kafafen watsa labarai daga Sifaniya da Slovenia da Ireland da kuma Netherlands suka bayyana bayan kaɗa ƙuri’ar cewa za su ƙurace wa Eurovision ta 2026.
Ce-ce-ku-cen na zuwa yayin da yaƙin da Isra’ila take yi a kan Gaza ke ci gaba duk da yarjejeniyar tsagaita wutan da Amurka ta jagoranta, yayin da adadin waɗanda ake kashewa cikin Falasɗinawa ke ƙaruwa kuma suka daga ƙasashen duniya ke ƙaruwa daga al’adu da kafafen watsa labarai da kuma ɓangarorin siyasa daban-daban.