| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan ceto masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su
Mutanen da aka ceto suna samun kulawa ta lafiya kafin daga bisani a hada su da iyalansu," in ji sakon shugaban.
Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron Nijeriya kan ceto masu yi wa kasa hidima da aka yi garkuwa da su
An kubutar da mutanen wadanda suka haɗa maza takwas da mata 13 daga dazuzzukan Ofu a ranar Linitin.

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya jinjina wa jami’an tsaron kasar kan ceto mutane 21, ciki har da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) 15 da kuma wasu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi.

Shugaba Tinubu ya tabbatar da hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yammacin ranar Litinin, inda ya ce haɗin gwiwar aikin tawagar bincike da ceto (SAR) wanda ya haɗa dakarun soji da jami'an 'yansandan da ma'aikatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya da kuma 'yan banga na yankin ne suka kai ga ceto dukkan wadanda aka sace.

An kubutar da mutanen wadanda suka haɗa maza takwas da mata 13 daga dazuzzukan Ofu a ranar Litinin.

"Masu yi wa ƙasa hidima da sauran waɗanda aka ceto suna samun kulawar lafiya kafin a haɗa su da iyalansu," in ji sakon shugaban.

"Yayin da aka ceto wadanda aka sace lafiya, har yanzu jami'an tsaronmu masu kwazo suna kan hanyarsu ta farautar masu garkuwa da mutanen, bisa ga umarnin da na bayar na ci gaba da matsin lamba ga dukkan masu aikata laifuka," in ji Tinubu

Yana mai kari da cewa “waɗanda ke da alhakin wannan aika-aikar za su fuskanci cikakken hukuncin doka, kuma hukumomin tsaronmu za su bi duk wanda ya taimaka ko yake da hannu a wannan laifin.’’

’’Gwamnatina za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya zai iya yin tafiya a faɗin ƙasarmu ba tare da tsoro ba.”

Ya jinjina wa tawagar haɗin gwiwar saboda jajircewarsu, kana ya yaba wa iyalai da abokan arziki waɗanda aka sace saboda fahimtarsu a yanayin mummunar kaddarar da fada kan ‘yan’uwansu.

Yayin da yake nuna farin ciki da jinjinar iyaye da abokan arziki na waɗanda aka ceto, Shugaban ya tabbatar musucewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron rayukansu da dukiyoyinsu, da kuma na sauran 'yan Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutanen ne da misalin ƙarfe 4:40 na yamma a ranar 26 ga Agusta, kusa da mahadar hanyar Ogene Zaria-Onicha-Igo.

'Yan sanda sun ce ‘yan bindigan sun fito ne daga daji kana suka tare motocin bas guda biyu da ke tafiya zuwa wurare da daban-daban.

Kazalika sun sace wasu fasinjoji yayin da wasu suka tsere zuwa cikin daji da ke kewaye da wurin.