Rundunar Hisbah ta jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta ce jami’anta sun fara kama mutanen da ba sa azumin watan Ramadan.
Mataimakiyar kwamandan rundunar, Malama Ummakulsum Kassim ta shaida wa TRT Afrika cewa tuni suka kama mutum takwas da ba sa yin azumin ba tare da wata kwakkwarar hujja da Musulunci ya bayyana ba.
Ta kara da cewa bayan sun kama mutanen da ke cin abinci a bainar jama’a suna mika su ga hukumomi idan suka tabbatar sun taba akata laifin a baya.
A cewarta, cikin wadanda suke kamawa har da mata saboda a kan samu wasu maza da ke daukarsu su ba su kudi da abinci don yi wa Hisbah shagube.
Tun da farko, a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, rundunar ta ambato kwamandanta Harun Ibn-Sina yana gargadin wadanda suke yin ayyukan alfasha a wannan wata mai albarka da su daina.
“Za mu hukunta matasan da ke cin abinci a bainar jama’a,” in ji Harun Ibn-Sina.
Ya kuma yi kira ga dukkan Musulmai da su taimaki mabukata da marayu a wannan wata.







