Majalisar dokokin Ghana za ta kada kuri’a kan tantance ministoci
Kakakin Majalisar Alban Sumana Kingsford Bagbin, ya ce za a kada kuri’a kan batun amincewa da sabbin ministocin a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris.
Majalisar dokokin Ghana za ta tantance sababbin ministoci a ranar Juma'a, a cewar kamfanin dillancin labarai na kasar.
A kwanakin baya ne majalisar ta gaza cimma amincewa da sunayen da aka gabatar musu, duk da cewa an tafka muhawara a zauren majalisar.
Yayin da yake yanke hukunci kan kudurin amincewa da sunayen ministocin, Kakakin Majalisar Alban Sumana Kingsford Bagbin, ya ce za a kada kuri’a kan batun amincewa da sabbin ministocin a ranar Juma’a, 24 ga watan Maris.
Sunayen da ake tantancewa su ne Mr Kobina Tahir Hammond a matsayin minista a Ma’aikatar Kasuwanci da Kamfanoni da Mr Bryan Acheampong, minista a Ma’aikatar Abinci da Noma, da Mr. Stephen Asamoah Boateng, minista a Ma’aikatar Harkokin Sarautun Gargajiya da Addini.
Sauran ukun su ne Dr Mohammed Amin Adam, karamin minista a Ma’aikatar Kudi, da Mr Osei Bonsu Amoah, karamin minista a Ma’aikatar Kananan Hukomomi, Yada Ayyukan Gwamnati da Cigaban Karkara, da kuma Dr Stephen Amoah mataimakin minista a Ma’aikatar Kasuwanci da Kamfanoni.
Majalisar ta Ghana ta riga ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan batun a ranakun 20 da kuma 21 ga watan Fabrairu.
Sannan kafin haka, wadanda ake nema su zamo ministocin sun bayyana gaban kwamitin da ke kula da nade-naden ministoci, wanda ake kira da Kwamitin Kudurcewa da Nadawa.
Shugaban kwamitin majalisar, Mr Joseph Osei-Owusu, wanda kuma shi ne mataimaki na farko na Kakakin Majalisar, ya tabbatar wa da majalisar cewa kwamitin nasa ya tantance duka mutanen.
Sakamakon haka, ya bayar da shawara ga majalisar ta amince da rahoton kwamitin nasa, na cewa a karbi kudurin nada ministocin.
A yanzu dai ana dakon ganin ko kada kuri’ar zai sa majalisar ta amince da sunayen ministocin, ganin cewa wasu ‘yan majalisar sun soki yunkurin kara yawan ministocin Shugaba Nana Akuffo-Addo, da suka kira mai “matukar yawa”, saboda ta kunshi sama da 80.