'Yan sanda sun fi caje yara babaken fata a Ingila da Wales - Rahoto

Rahoton ya nuna cewa kimanin yara 2,847 ‘yan tsakanin shekara 8 zuwa 17 ne aka caje karkashin ikon tsayar da mutum a bincike shi da ‘yan sanda ke da shi.

By Abdulwasiu Hassan
Rahoton ya ce ya kamata a yi wa dokar caje mutum na Birtaniya garam bawul/Photo AA / Others

An fi caje yaran bakaken fata sau shida fiye da sauran yaran a Ingila da kuma Wales, in ji wani bincike da kwamishinan yara na Ingila ya fitar.

Rahoton wanda ya dogara kan bayanan da aka samu kan wadanda ‘yan sandan Birtaniya suka caje a Ingila da Wales tsakanin shekarar 2018 zuwa 2022, ya fito ne daga nazarin da kwamishinan yara na Ingila ya yi.

Rahoton ya nuna cewa kimanin yara 2,847, ‘yan tsakanin shekara 8 zuwa 17 ne aka caje karkashin ikon tsayar da mutum a bincike shi da ‘yan sanda ke da shi.

Kimanin kashi 95 cikin 100 na yaran maza ne, yayin da kashi 38 cikin 100 na yaran da aka caje babaken fata ne.

Rahoton ya nuna damuwa cewar an gudanar da kashi 52 cikin 100 na binciken ba tare da kasancewar “babba da ya dace a wajen ba.”

An bayyana “babba da ya dace” a matsayin iyaye ko uban riko ko ma’aikaci ko kungiyar agaji ko kuma wani wakilin hukuma wanda yaron yake karkashin kulawarsa.

Ba a dauki bayanin kimanin kashi 45 cikin 100 na wuraren da aka yi binciken ba. Sai dai kuma kashi 37 cikin 100 na binciken ya faru ne a ofishin ‘yan sanda kuma kashi 12 cikin 100 na binciken ya faru a gida.

A kalla an yi caji 14 a cikin motar ‘yan sanda ko kuma a maranta. An yi kimanin kashi 6 cikin 100 na binciken ne a gaban wani ko wata ‘yar sanda wanda jinsinta ba daya ne da wanda ake bincike akai ba, in ji rahoton.

Rahoton ya kara da cewa, kimanin kashi 51 cikin 100 na binciken bai gano komai ba.

Rahoton ya ba da shawara cewar Ma’akatar Harkokin Cikin Gida ta Birtaniya ta yi garam bawul wa dokar da ta shafi bincike kan yaran da ke karkahin kulawa da kuma bincike na kan hanya.