Duk da mummunar girgizar kasa da Turkiyya ta yi fama da shi, cikin watan Maris kasar ta samu karin dala biliyan 23.6 na kudin kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje, da kusan karin kashi hudu cikin 100 na abin da take samu a duk shekara, a cewar Ministan Harkokin kasuwancin kasar Mehmet Mus a ranar Talata.
Tagwayen girgizar kasar sun auku ne a farkon watan Fabrairu a wasu yankuna 11, kuma rabon da wadannan yankuna ke fitarwa gaba daya a kasar ya kai kashi takwas cikin 100 a shekarar 2022, in ji Mehmet Mus a wani taron manema labarai a da aka gudanar a Istanbul.
Kazalika kudaden kayayyakin da Turkiyya ke shigowa da su ya karu a cikin watan da kashi hudu cikin 100 a cewar Mehmet Mus.
Ma'aunin cinikayyar kasashen waje na Turkiya ya nuna gibin dalar Amurka biliyan 8.26 a cikin watan, kamar yadda alkaluman kungiyar masu fitar da kayayyaki ta kasar TIM ya nuna.
A halin da ake ciki, kayayyakin da Turkiyya ta fitar a cikin rubu'in farkon shekarar nan sun kai dala biliyan 61.6, adadin da ya karu da kashi 2 cikin 100.
Yayin da kayayyakin da ake shigowa da su kasar suka karu da kashi 11 cikin 100 wanda ya kai dala biliyan 96.5, in ji Mus.
A alkaluman da TIM suka fitar ya yi nuni da cewa an samu tazarar dala biliyan 34.9 na kudaden cinikayya da kasashen waje a rubu'in farko na wannan shekara.
Bayanan alkaluman ya yi kari da cewa Jamus ce kasar da Turkiyya ta fi fitar da kayayyakinta a watan Maris inda ta samu dala biliyan biyu sai Amurka da ke biye mata da dala biliyan 1.38 sai kuma Italiya da dala biliyan 1.19
Manyan kasashen da aka fi shigowa da kayayyaki Turkiyya a watan Maris sun hada da Rasha wacce aka fitar da dala biliyan 3.99, sai China da dala bilyan 3.78 sai kuma Jamus da dala biliyan 2.69.
Jimillar kayayyakin da kasashen Kungiyar Turai EU suka shigo da su Turkiyya sun kai dala biliyan 9.76 a watan Maris, yayin da kayayyakin da aka fitar daga Turkiyya suka kai dala biliyan 10.12.











