Altun: Turkiyya ta zama abun misali ga duniya kan magance ibtila’o’i
Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya bayyana cewa bayan afkuwar girgizar kasar da ta yi ajalin sama da mutum 50,000 a ranar 6 ga Fabrairu, Turkiyya ta zama abin misali ga duniya wajen kula da magance ibtila’o’i
Daraktan na Sadarwa na kasar ya ce Turkiyya ta zama abin misali ga duniya wajen magance ibtila’o’I da nuna karfafa gwiwa.
Altun ya sanar da hakan a wajen Babban Taron Hadin Kai da Goyon Baya Yayin Ibtila’o’I da aka gudanar a Ankara babbanb birnin Turkiyya.
Altun ya kara da cewa wannan taro zai yi duba kan hanyoyin inganta bayar da taimako, hadin kai da goyon baya a lokutan da ibtila’I ya afku a wani yanki na duniya.
Ya kara da cewa duniya na fuskantar hadurran da sun fi karfin a ce kasa daya kawai suka shafa kamar matsalar tattalin ariki, yake-yake, annoba da sauyin yanayi.