Shirin rusa rundunar sojin Amhara ya janyo mummunar zanga-zanga a Habasha
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fada a wata sanarwa sun fito da shirin ne domin hada kan ‘yan kasar Habasha.
Wasu 'yan kasar Habasha sun bayyana cewa an ji karar harbe-harbe a akalla a garuruwa biyu na yankin Amhara, yayin da dubban mutane suka yi zanga-zangar nuna adawa da umarnin gwamnatin kasar na hade rundunonin soji na lardunan kasar cikin rundunar soji ta kasa.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fada a wata sanarwa cewa Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya fada a wata sanarwa sun fito da shirin ne domin hada kan ‘yan kasar Habasha, kuma zai shafi duka lardunan kasar guda 11, wadanda suke da rundunonin sojin na kansu.
Wani mazaunin garin Gondar, inda aka yi gagarumar zanga-zanga ranar Lahadi, ya ce mambobin runduna ta musamman ta Amhara, sun yi ta harba makamansu sama, tsawon dare don nuna kin amincewarsu da umarnin na gwamnati.
Mutane biyu mazauna garin Kobo sun ce sun ji karar atilari a wajen garin. Amma ba a tantance su waye suka yi barin wutar ba.
An samu karin zanga-zanga a akalla garuruwa shida daban, kamar yadda wasu mazauna yankin suka ce. Sai dai ba su yarda a ambaci sunansu ba saboda tsaron kansu.
Amma ba a iya jin ta bakin masu magana da yawun gwamnatin Habasha, ko na rundunar soji, ko kuma na gwamnatin Lardin Amhara ba.
Mambobin rundunar soji ta musamman ta Amhara, da kuma gamayyar masu dauke da makamai a yankin suna adawa da wannan umarni na gwamnatin tarayyar kasar.
Wannan wani karan tsaye ne ga gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed, wanda ya fada a wata sanarwa cewa manufar shirin shi ne “hada kan al’ummar kasar”.
Umarnin zai yi aiki ne larduna 11 na kasar, wadanda suke da rundunonin soji, da kuma ‘yancin amfani da harshensu.
Nuna adawa da shirin ya fi kamari a Amhara, birni na biyu mafi girma, inda aka fara takun-saka da Firminista Abiy Ahmed a baya.
Wata kafar labarai da ke karkashin gwamnatin lardi ta Ambato shugaban Amhara Yilkal Kefale yana cewa, an yi wa umarnin na gwamnatin tarayya gurguwar fahimta mai nuna ana so ne a rusa rundunar soji ta musamman ta yankunan kasar.
An kuma Ambato shi yana cewa, a zahiri umarnin yana neman a tsara rundunonin larduna ne karkashin hukumomin tsaro na tarayya.
Tararrabi na karuwa
Rundunoni na musamma da kuma kungiyoyi masu dauke da makamai sun yi yaki ne karkashin gwamnatin tarayyar Habasha tsawon shekaru biyu da ta gwabza yaki da yankin Tigray mai makotaka.
Rikicin ya zo karshe ne sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi a watan Nuwamban da ya gabata, bayan da aka kashe dubban mutane.
Sai dai a ‘yan watannin nan, shugabannin Lardin Amhara da ‘yan fafutuka sun zargi gwamnatin Abiy Ahmed kan yin burus da zaluncin da aka yi wa ‘yan asalin Amhara da suke rayuwa a yankin Oromiya.
Sun kuma zargi gwamnatin da shirin mayar wa da Tigray yankunan da aka kwato daga gunsu lokacin yakin.
Sun ce idan aka rusa rundunonin lardin nasu, za su fuskanci hadarin farmaki daga Tigray da Oromiya.
Sai dai mai magana da yawun gwamnati bai amsa tambayar da aka tura masa ba don neman jawabi kan batun.